Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

0
48

Sojojin Najeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce, MNJTF, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.

An bayyana nasarar ne ‘yan sa’o’i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja.

Aikin da Brig. Gen Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.

Wata majiyar soji ta fadawa PRNigeria cewa sansanonin sun kasance sansanin horar da mayakan kungiyar tare da girke dakaru masu shirin ko-ta-kwana a shirye-shiryen kai harin kwanton bauna a wuraren sojojin da ke kusa.

Majiyar ta ce an kashe wasu kwamandojin kungiyar ‘yan ta’addan da kuma mayaka masu yawan gaske, yayin da yawa kuma suka samu munanan raunuka yayin kai harin.

Sojojin Najeriya sun mamaye sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa

An kame dimbin kayan aiki daga hannun ‘yan ta’addan yayin da kayan abinci, Na’urar abubuwan fashewa, Bama-bamai, abubuwan dinkin kayan sawa duk an lalata su.

Hausawa mutanen kirki ne, Fulani ne matsalan Najeriya – Nnamdi Kanu

“Mun share Maiyanki, Darulsallam, Bula kurege kuma yanzu mun karbe Izza, dukkansu tsoffin wuraren Boko Haram ne masu karfi. Sojojinmu sun sha kai hari mafakarsu, cikin dare, amma duk an fatattake su yayin da aka yiwa makiyan mummunar rauni.

Ya kuma bayyana cewa soja daya ne ya rasa rayuwarsa yayin da sojoji uku suka ji rauni.

A wani labarin, Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) ta ba da sanarwar buɗe kofarta don shiga cikin kwas na 73 na yau da kullum.

Masu sha’awar neman shiga makarantar na iya nema daga 23 ga Janairu zuwa 24 Afrilu, a cewar Magatakardar Makarantar, Brig.-Gen Ayoola Aboaba.

Aboaba, a cikin wata sanarwa a daren Lahadi, a Kaduna, ya ce an bude karbar shiga ne ga duk wadanda suka cancanta maza da mata ‘yan Najeriya.

What's On Your Mind?