Sojoji sun hallaka yan ta’addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7

0
17

Hukumar Sojin Najeriya ta alanta samun nasara kan yan ta’addan Boko Haram (ISWAP) da suka yi kokarin kaiwa Sojoji hari a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

Diraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Bernard Onyeko, ya bayyana cewa Sojoji sun samu nasarar hallaka adadin yan ta’addan mai yawa.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7

Bernard Onyeko yace “rundunar Operation TURA TA KAI BANGO tare da hadin kan mayakan saman Operation LAFIYA DOLE sun ragargaza motocin yakin Boko Haram/ISWAP tare da kashe adadi mai yawa cikinsu yayinda sukayi kokarin kai hari insa suke a Marte.”

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna

Ya ce sojojin sun yiwa yan ta’addan kwantan bauna “inda suka bude musu wuta kuma aka samu nasarar nan”

Kalli hotunan:

Kun ji cewa yan ta’addan ISWAP sun kai hari, da yammacin Juma’a, barikin Sojoji dake Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa har da safiyar Asabar suna cikin barikin.

Wannan hari na zuwa ne lokacin da gwamnatin jihar Borno ke shirin mayar da mutane 300 garin. A Oktoban 2020, gwamnan jihar ya kaddamar da kwamitoci biyu domin mayar da yan sansanin yan gudun Hijra Marte, Kirawa da Ngoshe.

 520 total views,  6 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here