Sojoji sun hallaka Kwamandoji 2, Boko Haram sun yi wa shugabansu mummunan juyin-mulki

0
46

A yunkurin da dakarun hadin-gwiwa su ke cigaba da yi na ganin bayan ‘yan ta’adda, sun halaka wasu manyan jagororin kungiyar Boko Haram.

Sojoji sun hallaka Kwamandoji 2, Boko Haram sun yi wa shugabansu mummunan juyin-mulki

Tallan Shirin Farin Wata Sha Kallo na Adam A zango Da Yasa Yar Ummi Rahab Hausa Series

Jaridar PRNigeria ta fitar da rahoto cewa sojojin MNJTF sun yi samame a ranar Juma’a, 29 ga watan Junairu, 2021, inda su ka samu galaba a kan Boko Haram.

Rahoton ya tabbatar da cewa a wannan samame da aka kai, sojojin sun hallaka wasu manyan jagororin Boko Haram biyu; Alai Bor da Maleum Modu.

Bayan haka, sojojin sun kashe mayakan kungiyar ta’addan Boko Haram a yankin na Arewa maso gabas.

Dakarun Najeriya da hadin gwiwar MNJTF sun kashe Alai Bor, shugaban Boko Haram a kauyen Buwari, a garin Bama, yayin da yake yunkurin tsallaka wa Gwoza-Pulka.”

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar hallaka wasu mayaka shida da ke cikin tagawar Amir Bor.

“Sauran jagororin ‘yan ta’adda, Maleum Modu da kuma mayakan Boko Haram uku sun mutu a hannun dakarun sojojin da ke sintiri a yankin Mafa.”

Hakan na zuwa ne bayan wasu mayakan ta’addan sun yi juyin-mulki, sun hambarar da gwamnatin Amir Abbah-Gana Tumbum Kayowa, inda aka yi jina-jina.

‘Yan ta’addan sun kifar da Abbah-Gana ne bayan zanga-zangar da aka yi masa a dalilin nada Aliyu Chakkar da ya yi a matsayin gwamnan Tafkin Chadi bayan Goni Maina.

Kwanakin baya kun samu rahoto cewa daga zuwa gidan biki, miyagu masu satar jama’a sun yi garkuwa da wasu matasa 25 a karamar hukumar Takum, Jihar Taraba.

Wadannan ‘yan bindiga sun ce sai an biya Naira Miliyan 50 za a fito da wadannan matasa da aka sace a hanyar zuwa biki, inda aka bukaci kowa ya biya miliyan biyu.

Daga baya an fito da duka wadannan Bayin Allah, bayan sun shafe kwanaki kusan uku a tsare.

What's On Your Mind?