Sojoji Sun Ceto Dalibin Makarantar Coci Daga ‘Yan Garkuwa A Filato

0
83

Sojoji Sun Ceto Dalibin Makarantar Coci Daga ‘Yan Garkuwa A Filato

Dalibin ‘Calbary Worldwide Ministry’ da aka fi sanin makarantar da CAPRO, Kebin Eze, wanda masu garkuwa da mutane suka sace shi a ranar Alhamis din da ta gabata, ya samu kubutuwa bayan da sojoji suka yi kokarin ceto shi.

Majiyarmu ta nakalto cewa ‘yan bindiga solar mamaye makarantar da ke karamar hukumar Barikin Ladi a Jihar ta Filato da ke da nisan ‘yan kilomitoci da filin jirgin saman Yakubu Gowon Airport tare da yin garkuwa da dalibai guda biyu.

Sai dai daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din ya samu arcewa a lokacin da ya samu sarari bayan da jami’an tsaro suka kawo dauki tare da bude wa ‘yan bindigan wuta, wannan yanayin artabun ne ya baiwa daya daga cikin daliban daman arcewa, inda suka yi awun gaba da daya.

Sojoji solar ceto Eze ne a ranar Lahadi wanda dakarun OPSH Filato suka yi bayan samun bayanan ba tare da biyan ko sisi na fansa ba.

A sanarwar manema labarai da Kakakin rundunar OPHS Main Ibrahim Shittu ya fitar a Jos, ya ce, “Dalibin da muka ceto yana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma tunin aka maida shi cikin sauran dalibai ‘yan uwansa a makarantarsu.”

What's On Your Mind?