Sojoji Sun Ce Bisa Kuskure Suka Kashe ‘Ya’yana 2 Da ‘Yan Biki 3 – Malam Bello

0
118

Sojoji Sun Ce Bisa Kuskure Suka Kashe ‘Ya’yana 2 Da ‘Yan Biki 3 – Malam Bello

Daga Khalid Idris Doya

MALLAM BELLO ALIYU JEN wani tsohon ma’aikacin gwamnati ne a Jihar Taraba da sojoji suka kashe ‘ya’yansa biyu da wasu uku a lokacin wani bikin aure, ya shaida a hirarsa da jaridar Punch cewa sojojin solar bayyana masa cewa bisa kuskure suka kashe masa ‘ya’yan. KHALID IDRIS DOYA ya fassara mana zuwa Hausa. Ga hirar:
Ka gabatar mana da kanka?
Sunana Mallam Bello Aliyu Jen. Ni tsohon ma’aikacin gwamnatin Jihar Taraba ne kuma na fito ne daga karamar hukumar Ardo-Kola ta jihar.

‘Ya’yanka biyu na daga cikin biyar da aka kashe kwanan baya. Ya ne lamarin ya wakana?
Da karfe 2 na safiyar ranar 2 ga watan Afrilun 2021 daya daga cikin ‘ya’yana ya zo ya buga min kofa yake shaida min cewa ‘ya’yana wadanda ‘yan uwansa ne biyu an kashesu. Na tambayeshi cike da firgici, yaya kuma meye ya faru, sai dai ya nuna bai san hakikanin menene ya faru ba. A lokacin da ya je wajen da abun ya faru ne yake tabbatar min da cewa sojoji ne suka kashe yaran.
Da yake bayani bayanin kan gawar yaran, ya fadi min cewa sojojin da suka kashesu, solar kwashesu a cikin mota Hilus inda suka nufi Jalingo da su. Na fita domin na bi shi, sai yake ce min lamarin ya faru minita 30 da suka wuce ne, na ga sojojin da idona a cikin hilus din suna kokarin tafiya zuwa Jalingo. Na bi su zuwa asibitin FMC da ke Jalingo amma solar hana mutane zuwa kusa da su. Na yi yunkurin zuwa jikin motar da gawarwakin ‘ya’yana suke ciki.
Amma sai suka yi kokarin tsayar da ni, sai dai na fada musu, ban damu ba koda ni ma za su kasheni, don haka na bi ‘ya’yana kawai nima. Nan sai sojojin suka amince na je domin na duba gawar ‘ya’yan nawa. A lokacin da na isa ga hilus din, na ga ‘ya’yana biyu, Abdulkadir Bello, dabilin ajin karshe a kwalejin ilimin gona ta Jalingo da Tukur Bello, wanda kwanan nan ya gama sakandari a shekarar da ta gabata. Da na ga gangan jikinsu (Gawa), na kadu sosai nan dai fara kuka. Sojojin sau suka fara bani hakuri, suka ce min wai solar kashe yaran ne bisa kuskure.
Na tambayesu, wani irin kuskure ne kuka aikata haka na kashe min ‘ya’ya biyu da wasu uku? Sai dai solar kasa bani wannan amsar.
Na sake tambayarsu ko za su bani makaman da suka samu yaran da su solar kasa kawo min ko daya. Bayan duk wannan solar tafi da gawarwakin. Ni kaina da iyayen sauran yaran da aka kashe mun bukaci a bamu gawarwakinsu domin mu yi musu jana’iza sai aka umarce mu da mu koma karamar hukumar Ardo-Kola domin ganawa da DPO a wajen. Mun je din mun yi ta kokarin ganinsa har zuwa 4pm daga baya aka sake mana gawarwakin. Mun je muka dauki gawarwakin muka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Mene ne hukumomin soji suka bayyana kan wannan lamarin?
Kamar dai yadda na fada maka tun farko, kai tsaye solar fada mana (Kisan nan) bisa kuskure ne suka aikata shi. Tun bayan wannan ba mu sake jin wani abu daga garesu ba kuma.

Mun iya fahimtar cewa akwai wasu da suka gamu da raunuka kan wannan harin. Me suka shaida maka na hakikanin abun da ya faru ne a wannan ranar?
Eh; katin gayyata ya batu a cikin al’ummar yankinmu na cewa akwai bikin auren Sule Soja a Garin Baka. Don haka, a wannan ranar ta daurin aure, su din (‘ya’yana da saura) solar nufi Garin Baka bayan da kudin hannunsu ya kare a yayin bikin, solar yanke shawarar dawowa gida. Suna da mashina hudu amma biyu ne suka rage sai daya ya dauko ‘ya’yana a kai. Mashinan na farko na biyu a lokacin da suka isa zuwa shingen binciken sojoji. Sojojin solar tsaida su suka nemi jin daga ina suka fito, solar shaida wa sojin cewa daga bikin aure suka fito. Sun nusar da sojojin zuwa ga kidan bikin auren daga wajen bikin ke fitowa wanda kai tsaye ke nuna daga inda suka fito kuma ana jin wakar daga wajen da aka tsayar da su.
Sun dai fada wa sojojin daga wajen biki suka dawo. A wannan yanayin ne sojojin suka fara harbi sama. A hakan wasu sojojin kuma suna kwanta suna harbi a lokacin da su kuma ‘ya’yan nawa ke tahowa zuwa shingen binciken hakan ya sanya suka bude musu wuta da kashesu. Bayan ‘ya’yana biyu, wasu uku su ma an kashesu, wasu matasan kuma solar tsira da harbin bindiga a jikinsu.

Wani yunkuri kuke na ganin adalci ya wanzu sakamakon kisan ‘ya’yanka?
Wadannan zaratan matasan da aka kashe min solar kasance jinshiki a gidana ba zamu tsura ido kawai mu bar jininsu ya tafi haka nan ba. Tabbas za mu garzaya kotu. Kuma muna da niyyar za mu je ga hukumar kare hakkin bil adama nan kusa, mu iyayen wadanda lamarin ya shafa za mu dauki mataki. Yanzu haka Lauyoyi solar rubuta wa hukumomin soji da sauran wadanda abun ya shafa, ina tabbatar muku za mu bi kadinmu.

What's On Your Mind?