Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da ‘yan bindiga a Katsina

0
109

A kalla dakarun sojoji shida ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gumurzun da suka yi da yan bindiga a kusa da Faskari Marabar Maigora da ke Jihar Katsina.

Yan bindigan sun kuma sace bindigu da harsashin sojojin da suka kashe.

Majiyoyi kwarara sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8.20 na safen ranar Lahadi yayin da dakarun sojojin suka yi yunkurin datse yan bindigan da ke hanyarsu na shiga daji.

“Sojojin ba su san cewa ‘yan bindigan sun girke wasu daga cikin mambobinsu a kan bishiyoyi kuma suka bude musu wuta. Daga bisani yan bindigan sun samu kwarin gwiwa suka bude wa sojojin wuta,” a cewar wani majiya wanda ke da bayani kan faruwar lamarin.

Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

Majiyar ya ce dakarun sojojin saman Najeriya, NAF, ne suka kawo wa sojojin dauki da jiragen su na sama inda suka tarwatsa yan bindigan.

An Rage Wa Babban Hafshin Soja mukami saboda ya fadi gaskiya Akan Yaki Da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya, a ranar Lahadi ta sanar da cewa dakarunta na Operation Hadarin Daji sun kashe a kalla yan bindiga 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, a cewar Hedkwatar Tsaro.

Hedkwatar ta Tsaro ta kuma ce sojojin sun kwato shanu 334 da yan bindigan suka sace daga hannun al’umma yayin gumurzun.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam’iyyar NPP da NDC kan wacce jam’iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri’a da ke zauren majalisar.

What's On Your Mind?