Sojin Najeriya sun mamaye garinsu ministan Buhari, suna zuba ruwan wuta

- Advertisement -

Sojin Najeriya sun mamaye garinsu ministan Buhari, suna zuba ruwan wuta

Yanzu haka sojojin Najeriya sun fara ayyukansu na binciko wasu ‘yan ta’adda da suka kai hari karamar hukumar Essien Udim dake jihar Akwa Ibom.

Ministan harkokin Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio dan karamar hukumar ne wacce jami’an tsaronta suka fuskanci wannan harin.

Dama a makonnin da suka gabata, ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun kai hari a jihohin kudu maso gabas da kudu-kudu.

Har yanzu dai minista Akpabio bai riga ya ce komai ba akan ayyukan da sojoji suke yi.

The Nation ta ruwaito yadda sojoji suka fara ragargazar duk wasu wurare da ake zargin maboyar ‘yan ta’adda ne a ranar Talata, 6 ga watan Afirilu.

An Yaba Wa TAJBank A Kokarinsa Na Bunkasa Bangaren Ilimi

Kamar yadda rahoton yazo, an turo jirage da dama don tabbatar da tsaro a yankin.

A ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu sojojin yankin suka umarci mazauna wurin da su yi gaggawar barin yankin don gudun kada wasu marasa gaskiya su boye a gidajensu.

Sai da aka kori dalibai daga jami’an Federal Polytechnic Ukana dake karamar hukumar Essien Udim wacce bata da nisa da gidan Akpabio don a samu a rufe makarantar.

A kalaman jami’in hulda da jama’a na sojin ya ce “Yanzu haka bamu san ko su waye ba, menene niyyarsu sannan kuma wanene ya turosu ba.”

A makon daya gabata, sai da suka kashe ‘yan sanda three, ciki harda wani CSP na ‘yan sanda bayan an kai musu hari har yanzu ba a san inda wasu four suke ba.

A wani labari na daban, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda aka ga wasu matasan jihar Kogi dauke da bulalai suna tsabga wa wasu matasa biyu da suke zanga-zangar nuna kiyayya ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A bidiyon wanda Premium occasions ta wallafa a ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu an ga matasan suna cire ‘Buhari Should Go’ daga jikin bango ana basgarsu da bulalai a mazaunansu.

Sun umarci matasan da su sake yin fenti a bango yayin da suke shan ruwan bulalai.

Supply: Legit

- Advertisement -