Siyasa Ce Ta Sa Hukumar Kwastam Kwashe Mana  Motoci 20 –MD Maslaha Motos

- Advertisement -

Siyasa Ce Ta Sa Hukumar Kwastam Kwashe Mana  Motoci 20 –MD Maslaha Motos

Ba Mu Karya Doka Ba Wajen Gudanar Da Aikinmu –Kwastam

Daga El-Zaharadeen Umar,

Jami’an hukumar ha fasa kwabri ta kasa kwastam solar sake yin dirar mikiya a kamfanin sai dai Motoci na Maslaha Motos mallakar shugaban jami’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu inda suka kwashe motoci guda 20 a daran shekarajiya

Baban Manajan darakta na kamfanin Muhammad Shu’aibu Shitu ne ya bayyanawa manema labarai haka a Katsina, inda ya ce abinda hukumar kwastam suke yi masu babu shakka rashin adalci ne kuma akwai sisaya a cikin wannan lamari.

“inason in tabbatar da duniya cewa shugaban hukumar Kwastam na kasa Kanal Hamid Ali mai Ritaya ya yi biki kuma za mu maida masa biki fiye da wannan ya yi mana, saboda mun gano cewa wasu ‘yan syasa ne suke amfani da shi wajan ganin sai ya tozarta mu kuma wallahi bai isa ba.” In ji shi

Haka kuma Alhaji Muhammad Maslaha ya yi zargin cewa babu abinda ke cikin wannan hukumar ta kwastam sai cin hanci da rashawa, amma ba a taba jin solar kama wani jami’in su ba solar kai shi kotu an hukuta shi ba, amma solar buge da kwashe masu motoci bayan solar biya harajin shigowa da motocin.

Maslaha yana mai cewa, jami’an kwastam din solar zo kamfanin Maslah Motos cikin dare wajan misalin karfe 1:30 da ke kan baban titi IBB inda suka rika harba bindiga ba ji ba gani, a ya yin da suka tsorota duk wasu yara da ke gadi a wajan sannan suka balla kofar suka yi amfani da karfi, suka kwashe motoci guda 20

Ya ce suna Allah wadai da wannan mataki da wannan hukuma ta dauka akan mai wannan kamfanin saboda kawai yana shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, ya ce ko shakka babu wasu ke amfani da shugaban hukumar wajan ganin an muzgunawa mai wannan kamfani kuma ba su isa ba a cewarsa.

“wani rashin adalci da wannan hukuma ta yi mana wanda nake son duniya ta sani shi ne, kimanin shekaru biyu da suka wuce, solar zo wannan kamfani solar kwashi motoci guda 7 sannan suka kamani suka tsare kar kwana tara, wanda hakan tasa na je kotu domin neman hakkina na keta alfarma ta da aka yi”

Ya cigaba da cewa, bayan solar ce sai mun biya haraji na naira miliyan 74 akan motoci 60 bayan duk mun biya masu obligation, amma suka ce wai wannan obligation na bogi ne , kuma su jami’an hukumar kwastam din suka yi mana shi, ya ce duk da haka solar amince za su biya wadannan kudade amma  sai gashi solar sake dawowa solar kwashe ragowar motoci 20 ciki har da wanda aka biya mata obligation a wajan su.

Sai dai kuma lokacin da muka tuntubi shugaban hukumar kwastam mai kula da jihar Katsina Dalha Chedi Wada ya tabbatar da faruwar lamari, inda ya ce solar gudanar da aikin su bisa ka’ida kuma an ba su umarni ne daga sama.

Haka kuma ya bayyana cewa duk wannan abun da ake magana abu guda biyu ne kawai, acikin shekarar 2019 solar kai samamaye a wannan kamfani solar kama wasu motoci guda 7 solar kai ofis din su, sannan solar dawo solar rufe wannan kamfani, saboda haka daga baya shugaban hukumar kwastam ta kasa Hamid Ali ya bada dama ga wannan kamfani da ya biya wasu kudade na obligation domin ya cigaba da wannan kasuwanci na shi.

“A maimakon haka, sai mai wannan kamfani ya bude wannan kamfani bayan hukumar kwastam ta rufe shi, yana karkashin ikonta, aka dauki motaci 27 daga cikin 52 da suka bari a ciki, wanda kuma yin haka laifi ne, sannan wannan kudadde da aka ce ya biya naira miliyan 74 ya ki biya kusan shekara biyu ke nan, saboda muke ganin kamar akwai raina hankalin gwamnati a cikin al’amarinsa” inji Dalha Wada

Sannan ya kara da cewa idan za su kai irin wannan farmaki ba su da bukatar sai solar samu iznin daga wata kotu ko wata hukuma, suna da cikakiyar damar da za su kaima ko ma wanene irin wannan samamaye akwai dokar da ta ba su wannan damar, ya kuma ce babu abinda zai ce dangane da batun akwai siyasa a cikin wannan al’amari, su ma’aikatan kaki ne ba ‘yan siyasa ba

Kwantorola Dalha Chedi ya ce bincike ya tabbatar masu da cewa kamfanin Maslaha Motos suna shigo da motoci ba bisa ka’ida ba, wannan tasa dole suka kai wa kamfanin farmaki saboda zargi da suke da shi, kuma doka ta ba su damar yin haka, akan kaya ko mota ko jirgin ruwa ko mutum ne ke tafiya a kasa idan baka amince da shi kana iya bincikarsa.

- Advertisement -