Sin Za Ta Kammala Aikin Gina Tashar Binciken Sararin Samaniya Nan Da Shekarar 2022

0
130

Sin Za Ta Kammala Aikin Gina Tashar Binciken Sararin Samaniya Nan Da Shekarar 2022

Daga CRI Hausa

Jiya Alhamis, Sin ta harba wani muhimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya mai suna Tianhe daga cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kasar Sin. Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan zirga-zirgar kumbon dake dauke da bil-Adama zuwa sararin samaniya na kasar Sin, Ji Qiming ya bayyana cewa, a bana, bi da bi, za a harba kumbuna masu dauke da kayayyaki guda biyu, da kumbuna masu dauke da mutane guda biyu, kuma, ya zuwa shekarar 2022, za a gama aikin gina tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin baki daya.
“An cimma nasarar harba muhimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya mai suna Tianhe.”
Jiya ne da misalin karfe 11 da mintuna 23, aka harba rokar CZ-5B dake dauke da wani muhimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya mai suna Tianhe, bayan dakika 494, kumbon Tianhe da rokar solar rabu, sa’an nan, ya shiga kama sararin samaniya kamar yadda aka tsara. Da misalin karfe 12 da mintuna 36, fikafikan kumbon guda biyu solar bude, suka kuma fara aiki kamar yadda aka tsara, daga bisani kuma, an sanar da cimma nasarar harbar kumbon Tianhe.
Kumbon Tianhe da aka harba a wannan karo, zai zama cibiyar tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, inda ‘yan sama jannati guda uku za su gudanar da gwaje-gwajen fasahohin sararin samaniya a ciki da wajensa.
Mataimakin shugaban tsara tsarin tashar binciken sararin samaniya Zhu Guangchen ya bayyana cewa, a cikin kumbon akwai dakunan kwana guda uku da na wanka guda daya, wadanda za su biya bukatun ‘yan sama jannati na rayuwar yau da kullum. Yana mai cewa, “A wurin cin abinci, akwai na’urar dumama abinci, da na’urar sanyaya kaya, da kuma na’urar samar da ruwan sha da sauransu, domin saukakawa ‘yan saman jannati a fannin abincin da za su ci. An kuma kebe na’urar motsa jiki da keke a cikin kumbon, ta yadda ‘yan sama jannatin, za su rika motsa jiki. An kuma tanadi na’urorin kunna da kashe fitilu na zamani, da fasahohin sadarwar WIFI, domin kara jin dadi ga ‘yan saman jannati yayin da suke cikin kumbon. Ta hanyar amfani da fasahar sadarwa da na’urorin yin hira ta bidiyo, ‘yan saman jannati za su iya yin hira ta bidiyo da mutane da ke duniyarmu.”
A yayin da yake tsokaci kan yanayin gina tashar binciken sararin samaniya, mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan zirga-zirgar kumbon dake dauke da bil-Adama a sararin samaniya na kasar Sin, Ji Qiming ya bayyana cewa, akwai matakai guda biyu recreation da gina tashar binciken sararin samaniyan, na farko shi ne gwaje-gwajen fasahohin da abin ya shafa, na biyu shi ne, gina tashar. An tsara ayyukan harba kumbuna sau 12, kuma, ya zuwa shekarar 2022, za a gama ayyukan baki daya. Ya ce, ya zuwa yanzu, an riga an kammala ayyuka guda biyu a cikin muhimman ayyukan fasaha sau 6, a bana, bi da bi, za a harba kumbuna masu dauke da kayayyaki na Tianzhou guda biyu, da kuma kumbuna masu dauke da bil-Adama na Shenzhou guda biyu. Ya ce, “Muhimmin aikin dake gabanmu a matakin farko shi ne, gina tashar binciken sararin samaniya mai kunshe da bangarori guda uku cikin sararin samaniya. Za a harba wani kumbo mai dauke da kayayyaki kafin a harba kumbo mai dauke da bil-Adama, domin tabbatar da samun kayayyakin da ‘yan sama jannati suke bukata. A cikin ko wane kumbo mai dauke da bil-adama, akwai ‘yan sama jannati guda uku, wadanda za su yi aiki a sararin samaniya na watanni three zuwa watanni 6. Kana, a yayin da suke ayyuka a cikin sararin samaniya, za su rika jigilar kayayyaki, da gwaje-gwajen tsarin kare rayuwa, da aikin gyara, da kuma wasu ayyukan da za a gudanar a wajen kumbo, da wasu gwaje-gwajen fasahohin sararin samaniya a fannoni daban daban da sauransu.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

What's On Your Mind?