Sin Tana Fatan Taron Kolin Kiwon Lafiya Na Duniya Zai Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tinkarar Kalubalen Duniya Bisa Tsarin G20

- Advertisement -

Sin Tana Fatan Taron Kolin Kiwon Lafiya Na Duniya Zai Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tinkarar Kalubalen Duniya Bisa Tsarin G20

Daga CRI Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru a yau cewa, Sin tana fatan taron koli na kiwon lafiya na duniya zai taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta bisa tsarin G20.

Rahotanni daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin na cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron, bisa gayyatar kasar Italiya mai shugabanci karba-karba na kungiyar G20 a wannan karo da hukumar gudanarwar kungiyar EU wadanda suka dauki bakuncin shiryawa tare ta kafar bidiyo.

Recreation da fatan Sin kan taron kolin, Zhao Lijian ya bayyana cewa, yayin aka sake samun yaduwar cutar COVID-19 a duniya, an shiga lokaci mai muhimmanci na hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da cutar. Sin tana fatan taron kolin zai taka muhimmiyar rawa, wajen tinkarar kalubalen da duniya take fuskanta bisa tsarin G20, da ci gaba da jagorancin hadin gwiwa wajen yaki da cutar a duniya, a matsayin wata alama ta kiyaye ra’ayin bangarori daban daban da yin hadin gwiwa da sauran kasashe, don kara yin imani ga kokarin kasashen duniya wajen cimma nasarar yaki da cutar nan da nan, da kyautata tsarin kiwon lafiya na duniya, da kuma raya sha’anin kiwon lafiyar bil Adam na bai daya. (Zainab)

- Advertisement -