Sin Ta Musanta Rahotannin Wasu Kafafen Watsa Labarai Game Da Gudummawarta Wajen Kandagarkin Annoba A Seychelles

- Advertisement -

Sin Ta Musanta Rahotannin Wasu Kafafen Watsa Labarai Game Da Gudummawarta Wajen Kandagarkin Annoba A Seychelles

Daga  CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta musanta wasu rahotanni da wasu kafofin watsa labarai suka fitar, suna masu cewa rigakafin kasar Sin da aka yi amfani da shi a kasar Seychelles bai yi tasiri ba.

Da take musanta rahotannin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, a yau Laraba, Hua ta ce tuni shugaban Seychelles ya karyata wadancan rahotannin, ya kuma ce rigakafin kasar Sin ya yi matukar taimakawa wajen yaki da annobar a Seychelles.

Jami’ar ta kara da cewa, a kwanakin baya, mujallar “The Wall Road” ta wallafa wasu makalu masu nasaba da yanayin da ake ciki sport da cutar COVID-19 a Seychelles, inda mujallar ta aza ayar tambaya sport da tasirin rigakafin COVID-19 samfurin kasar Sin.

Cikin martaninta, Hua Chunying ta kara da cewa, wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya, har kullum na fatan kushe inganci da nagartar rigakafin kasar Sin, suna kuma yada jita jita da karairayi sport da kasar Sin, wanda hakan ke bayyana mummunar aniyar su, ta shafawa kasar Sin kashin kaji.

Dangane da hakan, shi ma shugaban kasar Seychelles Wavel Ramkalawan, ya maida martani ta cikin wata sanarwa, yana mai cewa mafi yawan sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19 a Seychelles ba su karbi rigakafin cutar ba, kuma ba a samu rasa rayuka tsakanin wadanda suka karbi rigakafin zagaye 2 ba. Don haka fannin magungunan kasar Sin na da inganci, ya kuma samarwa al’ummar Seychelles hidima mai gamsarwa. (Saminu)

- Advertisement -