Sin Ta Kaddamar Aikin Ba Da Horo Na Luban A Habasha Don Bunkasa Sana’o’i

0
61

Sin Ta Kaddamar Aikin Ba Da Horo Na Luban A Habasha Don Bunkasa Sana’o’i

A ranar Laraba kasar Sin ta kaddamar da shirin ba da horo na Luban da nufin samar da kwarewa ga daliban da suka kammala karatu, don taimaka musu wajen samun kwarewar aikin da ake bukata a kasuwannin neman guraben ayyukan yi.
An shirya taron ba da horon ne a jami’ar kimiyya ta Habasha (ETU) dake babban birnin kasar Addis Ababa, wanda jami’ar fahasa ta Tianjin ta kasar Sin (TUTE) ta kafa, karkashin ma’aikatar ilmi ta kasar Sin.
Da yake jawabi a bikin kaddamar da shirin ba da horon na Habasha Luban, Teshale Berecha, shugaban jami’ar ta ETU, yace, aikin ba da horon wanda jami’ar ilmin fasaha ta kasar Sin TUTE ta shirya karkashin jami’ar ta ETU ta Habasha, zai inganta yanayin aikin koyarwa a fannonin ilmin fasahar kere-kere, da fasahar mutum-mutumi da fasahar kwaikwayon tunanin dan adam ta AI.
Tun bayan gudanar da aikin ba da horon Luban na farko a Afrika, wanda aka gudanar a kasar Djibouti a watan Maris na shekarar 2019, akwai kasashen Afrika da dama kamar Najeriya, Kenya da Uganda wadanda suka kaddamar da aikin ba da horon na Luban da nufin samar da kwarewa a fannin koyar da sana’o’i ga mutanen kasashensu, musamman matasan kasashen.(Ahmad)

What's On Your Mind?