Sin Ta Bukaci Australia Da Ta Martaba Ci Gaban Sin Da Ma Alakarsu Bisa Adalci

- Advertisement -

Sin Ta Bukaci Australia Da Ta Martaba Ci Gaban Sin Da Ma Alakarsu Bisa Adalci

Daga CRI Hausa

Kasar Sin ta bukaci kasar Australia, da ta yi watsi da ra’ayi na cacar baka, da tunani na son zuciya, ta kalli ci gaban kasar Sin da ma alakarsu da idon basira, ta kuma daina siyasantar da musayar dake tsakanin kasashen biyu.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, shi ne ya bayyana haka, Alhamis din, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa. A yau ne kuma, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin, ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ta ce, daga yau ta yanke shawarar dakatar da duk wasu ayyuka karkashin tattaunawar tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Australia har sai illa masha allahu. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

- Advertisement -