Sin Na Tsaiwa Tsayin Daka Wajen Ingiza Zumunci Tsakaninta Da Kasashen Afirka

- Advertisement -

Sin Na Tsaiwa Tsayin Daka Wajen Ingiza Zumunci Tsakaninta Da Kasashen Afirka

A ranar 25 ga watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a cibiyar taron kasa da kasa na Nyerere dake kasar Tanzaniya, inda ya gabatar da manufar nuna gaskiya da aminci wajen gudanar da huldar dake tsakanin kasarsa da kasashen Afirka, da ra’ayin samun moriya bisa adalci, wadanda suka ba da jagoranci ga ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki.

Bana shekara ce ta tabbatar da sakamakon da aka cimma, a yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka da aka kira a shekarar 2018, kuma shekara ce da sassan biyu za su tsara sabon shirin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu a nan gaba. To shin ko ta yaya manufar za ta ba da jagoranci wajen ciyar da huldar sada zumunta ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka daga duk fannoni?
An lura cewa, yayin da kasar Sin da kasashen Afirka suke gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, kan aikin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka allurar rigakafin cutar, da kayayyakin kiwon lafiya, tare da zumuncin al’ummun Sinawa.

A kwanakin baya, allurar rigakafin cutar COVID-19 ta kasar Sin sun isa kasar Comoros, inda shugaban kasar Azali Assoumani ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar wa kasarsa alluran kyauta, wanda hakan hakikanin mataki ne da ta dauka domin ingiza adalci yayin rarraba alluran rigakafin, lamarin da ya nuna zumuncin ‘yan uwantaka dake tsakanin al’ummomin Sin da Afirka, yana mai cewa, “Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Comoros, ya nuna manufar da kasar Sin take aiwatarwa a nahiyar Afirka, wato more fasahohi, da ilmomin kwarewar sana’o’in da ta samu tare da kasashen Afirka, kana kuma da samar da tallafi gare su. Yanzu haka mun samu allurar rigakafin kasar Sin, ta yadda za mu iya kaddamar da aikin yi wa al’ummun fadin kasar alluran. Ko shakka babu ni zan karbi rigakafin kafin sauran al’umma domin nuna misali.”

Wasu Kasashe Na Sa Ran Inganta Hadin Gwiwa Tare Da Kasar Sin A Fannin Yaki Da Cutar COVID-19

Shi ma shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya bayyana yayin da ya karbi zagaye na biyu na allurar rigakafin da kasar Sin ta samar, cewa tallafin kasar Sin zai daga matsayin kandagarkin cutar a Zimbabwe bisa babban mataki, a cewarsa: “Kasar Sin ta samarwa Zimbabwe goyon baya da tallafi ba tare da gindaya wani sharadi ba, musamman ma a lokacin da kasarmu take kokarin dakile matsalar yaduwar annobar. Ana iya cewa, tallafin kasar Sin ya rage matsin lambar da muke fuskanta, saboda hakan zai kara karfinmu na dakile annobar, kana zai kyautata rayuwar al’ummun kasarmu, har ma ya sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin kasarmu.”

A ranar 25 ga watan Maris na shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya bayyana a cibiyar taron kasa da kasa ta Nyerere dake kasar Tanzaniya cewa, Sinawa sun nuna sahihanci kan zumuncin dake tsakaninsu da al’ummun kasashen Afirka, kuma kasar Sin ta fi mai da hankali kan aikin daukar hakikanin matakai, yayin da take gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka.

Tsohon jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Afirka ta kudu, kuma wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka na farko Liu Guijin, ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu cewa, a ko da yaushe al’ummomin kasar Sin da na kasashen Afirka, sun kasance ‘yan uwa, ko sahihan abokai na samun ci gaba tare, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin sassan biyu ta samu ci gaba mai inganci, karkashin jagorancin manufar da shugaba Xi ya gabatar, yana mai cewa, “Ina ganin cewa, manufar nuna gaskiya da sahihanci, da ra’ayin samun moriya bisa adalci, sun yi bitar manufofin da kasar Sin ta dade ta na aiwatarwa a nahiyar Afirka, sun kuma ba da jagoranci a aikin gudanar da huldar sada zumunta dake tsakanin sassan biyu a karnin 21 da muke ciki.

Ana iya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ya samu babban sakammako karkashin jagorancin manufar.”
An lura cewa, a watan Maris na shekarar 2014, annobar Ebola ta bazu a nahiyar Afirka, kuma kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka kayayyakin kiwon lafiya cikin gaggawa, ta kuma aika jami’an kiwon lafiya da yawansu ya kai sama da 1000 zuwa ga kasashen. Kuma bayan annobar COVID-19 ta barke a kasar Sin, kasashen Afirka su ma sun nuna goyon baya gare ta.

Tsohon jakada Liu Guijin na da ra’ayin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, a fannin kandagarkin cutar COVID-19 ya nuna cewa, al’ummun sassan biyu abokai ne na gaske, wadanda ke goyon bayan juna, har a lokutan da suke fuskantar wahalhalu. (Mai fassaarawa: Jamila daga CRI Hausa)

- Advertisement -