Shugabannin APC Na Mazabar Zaitawa Sun Kori Danbilki Kwamanda Daga Jam’iyyar

0
100

Shugabannin APC Na Mazabar Zaitawa Sun Kori Danbilki Kwamanda Daga Jam’iyyar

Daga Ibrahim  Muhammad  Kano.

Jamiyyar APC rashen mazabar Zaitawa da ke yankin karamar hukumar birnin Kano ta kori Abdulmajid Danbilki Kwamanda daga matsayin Shugaban dattijai na mazabar Zaitawa Sannan  kuma ta dakatar da shi daga jamiyyar ta APC.

Wannan na kunshe ne cikin wata takarda dake dauke dasa hannun shugabannin jam’iyyar na mazabar Zaitawa.

Takardar ta ce, an  kafawa Danbiki Kwamandan kwamitin bincike saboda irin kalaman da yake yi na  batanci ga zabebbeben Gwamnan jihar Kano Dokta  Abdullah Umar Ganduje da iyalinsa da kuma suka ga gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari. Sannan solar zargi Danbilki da aiwatar da kalaman tunzura Jama’a kan  kada su  fito zaben kananan hukumomi daya gabata a Kano tare kuma  rattling cewar kada a zabi jamiyyar APC a yayin zaben.

Takardar Korar da da dakatar da Danbilkin ta sami goyan bayan kaso biyu cikin uku na shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Zaitawa Wanda Mataimakin shugaban mazabar Faruk shekarau ya sawa hannu.

 

Alhaji Abdulmajid Danbilki Kwamanda Wanda shugabancin APC na mazabar Zaitawa ta dakatar.

 

 

What's On Your Mind?