Shugaban Zimbabwe Ya Karbi Allura Ta Biyu Ta Rigakafin COVID-19 Ta Kamfanin Sinovac

0
70

Shugaban Zimbabwe Ya Karbi Allura Ta Biyu Ta Rigakafin COVID-19 Ta Kamfanin Sinovac

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya karbi allura ta biyu ta rigakafin COVID-19 ta kamfanin Sinovac na kasar Sin, jiya Alhamis a babban asibitin Kwekwe dake lardin Midlands.

Shugaba Mnangagwa ya karbi allurar ta farko ne a garin Victoria Falls a watan da ya gabata, inda ya samu rakiyar mataimakin shugaban kasar kuma ministan lafiya da kula da yara, Constantino Chiwenga, da ministan tsaro Oppah Muchinguri-Kashiri da wasu jami’an gwamnatinsa da dama.

Kasar Zimbabwe ta fara bayar da allurar rigakafin COVID-19 ne a ranar 18 ga watan Febreru, inda take da burin yi wa kaso 60 na al’ummarta da nufin samun mutane da dama masu karfin garkuwar yaki da cutar.
Zuwa yanzu, mutane 295,631 solar karbi allurar ta farko, yayin da 37,365 suka karbi ta biyu.

(Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?