Shugaban Sin Ya Jaddada Bukatar Gina Al’ummar Dake Jituwa Da Muhalli

0
70

Shugaban Sin Ya Jaddada Bukatar Gina Al’ummar Dake Jituwa Da Muhalli

Daga CRI Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya nanata bukatar daukar matakan raya zamantakewa da kiyaye muhalli ta hanyar zamanantar da tsarin jituwa tsakanin dan Adama da muhalli.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake jagorantar zaman nazari na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS a jiya Juma’a.

A jawabinsa, shugaba Xi ya ce, daya daga cikin sigogin tsarin gurguzu na zamani shi ne, jituwa tsakanin dan Adam da muhalli, yana mai kira da a gaggauta daidaita tsarukan amfani da masana’antu da makamashi da sufuri da filaye.

Ya ce, tabbatar da yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da kasar Sin za ta fitar zai kai matsayin koli kafin shekarar 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060, alkawari ne da kasar Sin ta yi a hukumance, kuma wani muhimmin sauyi ne mai matukar wahalar samu ga tattalin arziki da zamantakewa.

Ya ce wajibi ne a dakatar da duk wasu ayyukan dake bukatar makamashi mai yawa tare da fitar da hayaki mai guba. (Fa’iza Mustapha)

 

What's On Your Mind?