Shugaban NLC Ya Jagoranci Masu Zanga-zanga Zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna

- Advertisement -

Shugaban NLC Ya Jagoranci Masu Zanga-zanga Zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna

Daga Suleiman Ibrahim

Shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamared Ayuba Wabba, a yanzu haka yana jagorantar mambobin kungiyar kwadagon zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Wannan ya na zuwa ne biyo bayan da Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ana neman shugaban kungiyar da sauran shuwagabannin Kungiyar ruwa-a-jallo don zargin yiwa tattalin arzikin jiharsa zagon kasa da kai hari kan kayayyakin extra rayuwar jama’a.

Anga dimbin jama’a, a karkashin jagorancin Wabba, suna yin tattaki daga Waff highway da ke cikin garin Kaduna, sannan suka nufi gidan gwamnatin.

- Advertisement -