Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi Ya Yaba Wa Gwamna Bagudu Kan Kammala Aikin Hanya

- Advertisement -

Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi Ya Yaba Wa Gwamna Bagudu Kan Kammala Aikin Hanya

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Rt. Hon. Ismail Abdulmumin Kamba, ya yaba wa kokarin Sanata Abubakar Atiku Bagudu na kammala aikin titin mai tsawon kilomita 17 a yankinsa, a cikin halin durkushewar tattalin arziki kasa da na jihohi.

Aikin hanyar wanda ya fara daga garin Dole Kaina zuwa Tungar Rafi, a karamar hukumar Dandi, an kammala aikin cikin nasara kuma masu ababen hawa solar soma amfani da hanyar ,  Shugaban Majalisar ya bayyana hakan ne jim kadan bayan solar zagaya da Gwamnan a yankin nashi a jiya.

Rt. Hon. Kamba, wanda a bayaninsa ya yi farin ciki da ziyarar Gwamnan, don duba aikin da aka kammala, ya yaba wa Bagudu kan kammala daya daga cikin mahimman ayyukan titin a cikin jihar ta Kebbi.

Sabuwar hanyar da aka gina, a cewar shugaban majalisar, za ta bunkasa harkokin kasuwanci da noma a yankin.

‘Wannan aikin titin yana daga cikin  mahimmin aikin hanya, wanda yake da matukar mahimmanci ga rayuwar tattalin arziƙin jama’ar wannan yankin.

‘Hanyar mai tsawon kilomita 17 da aka gina a kan kudi naira Biliyan 1.four ba ta da tsada, domin, tana da manyan magudanan ruwa 40 da za su iya sauke yawan ruwan mutanen yankin, in ji shi”.

Ya kuma bayyana aniyar Gwamnan na hade hanyar daga Tungar Rafi zuwa Aljannare da ke a karamar hukumar Suru.

A nasa martanin, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa na ci gaba da kasancewa mai bayar da muhimmanci ga samar da muhimman ababen extra rayuwa, duk da karancin tattalin arziki da ake fama dashi.

Haka kuma Gwamna Bagudu ya yaba wa dan kwangilar kan nasarar kammala aikin da ya yi daidai da lokacin da aka shata masa, har ma da mawuyacin yanayin yankin da ke gefen kogin Neja.

Ya kuma yabawa dan kwangilar bisa kyakkyawan aiki da kammala aikin hanyar bisa kudin da aka amince da su.

Bugu da kari Gwamna  Bagudu ya taya shugabanni da mutanen yankin murna tare da tabbatar musu da cewa a shirye yake ya fadada hanyar daga Tungar Rafi zuwa Aljannare.

Daruruwan mazauna garin, wadanda suka hada da mata da yara, solar fito kwansu da kwarkwata don yiwa Gwamnan da sauran mukarraban sa murna yayin da suke bin hanyar domin dubawa.

Daga cikin manyan mutanen da suka rakiyar  gwamnan solar hada da Hon. Umar Abdullahi Zimbo, Dan majalisar  mai wakiltar mazabar Arewa da Dandi  a Majalisar Dokoki ta Tarayyar, Sarkin Shikon Kamba, Alhaji Mamuda Zarumai, Hakimin Kyangakwai, Alhaji Suleiman Musa da Hakimin Dole Kaina Alhaji Bello Marafa,

Sauran solar hada da Alhaji Sahabi Lolo, Mataimakin Shugaban riko na APC na Arewacin yankin Kebbi, Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Barista Attahiru Maccido, Kwamishinan Kasuwanci da Yawon Bude Ido, Garba Ibrahim Geza, Alhaji Ibrahim Bawa Kamba, tsohon Kwamishinan Kasuwanci da kuma Shugaban karamararamar Hukumar Dandi. , Garba Salihu Kamba Dila.

- Advertisement -