Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Ya Jajanta Wa Gwamnatocin Zamfara, Yobe Da Kaduna

0
101

Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Ya Jajanta Wa Gwamnatocin Zamfara, Yobe Da Kaduna

Daga Abubakar Abba

Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani ya jajanta wa Gwamnatocin Jihohin Zamfara, Yobe Kaduna da kuma alumomin su kan hare-hren da ‘yan bindiga suka kai a jihohin a kwanan baya, inda hakan ya janyo mutuwar wasu mutanen da dama.
Zailani wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabanin majalisun dokoki ta Arewacin kasar nan ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ya  sanyawa hanu ya kuma bai wa MOBILIZED9JA A Yau a Kaduna.
“Na kadu matuka kan hare-haren da aka kai a wadannan jihohin, a saboda haka, ina jajanta wa gwamnatocin jihohin da kuma alumomn su kan hare-haren”.
Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani ya kuma yi tir da harin da ‘yan kungiyar Boko Hram suka kai a karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Yusuf Zailani, ya kuma ya jajantawa iyayen daliban  jami’ar Greenfield uku da ke a jihar Kaduna da ‘yan bindga suka hallaka a yayin farmakin da suka kai jam’ar a makon day a gabata, inda kuma ya yi addu’ar fatan a sako sauran daliban jami’ar da har yanzu suke a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani ya kuma danganta harin na’yan bindiga a jami’ar ta Greenfield da ke a jihar Kaduna a matsayin farmaki kan ilimin Boko.

What's On Your Mind?