Shugaban Hukumar Tace Fina Finai Isma’il Afakallah Yayi Magana Akan Haukacewar Ashiru Nagoma

0
8

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu damar tattaunawa da fitaccen jarumi a masana’antar (Kannywood) Alhaji Ali Nuhu da kuma shugaban Hukumar Tace fina-finai na Jihar Kano, Ismail Na Abba Afakallah dangane da batun tsohon darakta, Ashiru Na Goma da ke fama da rashin lafiyar taɓin hankali a halin yanzu.

Shugaban Hukumar Tace Fina Finai Isma’il Afakallah Yayi Magana Akan Haukacewar Ashiru Nagoma

Shi ma a nasa tsokacin a ya yin tattaunawarmu da shi, shugaban Hukumar tace fina-finai na Jihar Kano, Ismail Na Abba Afakallah, ya bayyana cewa Ashiru Na Goma ya gamu da wannan iftila’i ne tun kafin shi ya hau kan wannan matsayi, kuma yanzu tunda har ƴan’uwansa solar amince a nema masa magani to za su kafa kwamiti na musamman a matsayin gidauniyar kulawa da Ashiru Na Goma.

Don Tabbatar Da Adalci A Tsakani Akwai Bukatar A Mikawa Kudu Mulki A 2023 ~ Zulum

Afakallah ya bayyana cewa Ashiru Na Goma ya ba da gagarumar gudunmawa ga masana’antar Kannywood a lokacin da ya ke da lafiya saboda haka a yanzu su ma za su yi iya ƙoƙarinsu domin ganin solar temaka masa.

Da ya ke tsokaci recreation da zargin da ake yi musu na ƙin taimakawa masu buƙata kuwa, Na Abba Afakallah ya bayyana cewa al’ada ce a wannan masana’antar kafa gidauniya domin tallafawa mutanensu da su ka gamu da jinya gami da tallafawa iyalansu “Ba ƴan fim kaɗai ba, har ma da mutanen gari mu na tallafa musu a lokacin da su ke buƙatar taimako. Misali, ko da Sani Garba SK mun kaiwa iyalansa gudunmawa, akwai mutane da dama da su ka gamu da jarrabawa a wannan masana’anta da wajenta kuma mun tallafa musu, al’amari ne idan ka yi saboda Allah ba dole sai ka faɗawa duniya ba”. Cewar Dakta Sarari.

Tunda farko, Afakallah ya bayyana cewa babu wani mutum da zai so wani ya shiga cikin wata jarrabawa. Daga ƙarshe ya kuma yi addu’a Allah Ya ba wa Ashiru Na Goma lafiya.

 303 total views,  3 views today

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here