Shugaban DRC Ya Yabawa hadin gwiwar Kasarsa Da Sin A Fannonin Hakar Ma’adinai Da Ababen More Rayuwa

- Advertisement -

Shugaban DRC Ya Yabawa hadin gwiwar Kasarsa Da Sin A Fannonin Hakar Ma’adinai Da Ababen More Rayuwa

Daga CRI Hausa

Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi, ya ce yana daukar dangantakar kasarsa da Sin da muhimmanci, kuma yana da niyyar zurfafa dangantaka da kamfanonin kasar Sin a fannin hakar ma’adinai da ababen extra rayuwa.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake rangadi a kamfanin hakar ma’dinai na Sicomines, wanda na hadin gwiwa ne tsakanin kamfanin Gecamines na Congo da wani rukunin kamfanonin kasar Sin, dake da mazauni a yankin Kolwezi na lardin Lualaba dake kudu maso yammacin kasar.

Shugaban ya kara da cewa, kasarsa ta kuduri niyyar daukaka hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasashen biyu, musamman a fannonin hakar ma’adinai da ababen extra rayuwa, ta yadda za a mayar da dangakantakar kasashensu biyu zuwa ta damarmakin samun ci gaba.

Ginin ababen extra rayuwa wani muhimmin aiki ne ga kamfanin Sicomines. Kawo yanzu, an kammala ayyukan extra rayuwa 31 da bangaren kasar Sin ya zuba jari, ciki har da hanyar sufuri ta Boulevard ta birnin Kinshasa. ( Fa’iza Mustapha)

 

- Advertisement -