Shugaba Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi Kan Harkokin Mata A Gun Babban Taron MDD

0
154

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a jiya 1 ga wata ta kafar bidiyo, a wajen babban taron MDD na tunawa da cika shekaru 25 da shirya babban taron mata na kasa da kasa a Beijing, inda ya gabatar da wasu muhimman shawarwari hudu, da jaddada bukatar taimakawa mata yaki da cutar COVID-19, da tabbatar da daidaiton jinsi, da inganta muhimmiyar rawar da mata suke takawa, tare kuma da fadada hadin-gwiwar harkokin mata a duk fadin duniya.

Shugaba Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi Kan Harkokin Mata A Gun Babban Taron MDD

Shugaba Xi ya ce, mata suna taimakawa sosai ga ci gaban zaman rayuwar alumma, inda suke bayar da gagarumar gudummawa a fannoni daban-daban. Ya ce yayin da ake kokarin ganin bayan cutar mashako ta COVID-19, akwai mata maaikatan jinya da dama da suka nuna himma da kwazo wajen yakar cutar.

Xi ya ce:

Ya kamata mu jinjina musu. Daga cikin maaikatan jinya sama da dubu 40 wadanda suka je yaki da cutar COVID-19 a Wuhan, sulusaninsu mata ne. Akwai wata nas yar kasa da shekaru 20, an tambaye ta, ke yarinya ce dake bukatar taimako, ta amsa cewa, idan na sanya rigar jinya, ni ba yarinya ba ce. Irin wannan furucinta yana sosa mana rai sosai.
A wajen taron, shugaba Xi ya bullo da wasu muhimman shawarwari hudu. Na farko, tallafawa mata yaki da cutar. Na biyu, tabbatar da daidaiton jinsi. Na uku, kara muhimmiyar rawar da mata suke takawa a wannan zamanin. Na hudu shi ne, inganta hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin harkokin mata.

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Makarantu

Xi Jinping ya bayyana cewa:

Ya dace kare hakkokin mata ya zama muradun kasa. A yayin da ake samun farfadowa bayan annobar, ya kamata a samarwa mata sabon zarafin shiga fagen siyasa, da kawar da bambancin ra’ayi da wariyar jinsi da ake nuna musu.”
Shugaba Xi ya kara da cewa, kamata ya yi a kara himmantuwa wajen kare hakkokin mata, da kyautata zaman rayuwarsu, ta yadda za su kara jin dadin rayuwa.

Xi ya jaddada cewa:

“Muna goyon bayan MDD don ta sanya harkokin da suka shafi mata a gaba da kome, da kara zuba kudi a fannonin kawar da ayyukan lalata, da nuna bambancin ra’ayi da kuma zaman talauci.”

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, tabbatar da daidaiton jinsi wata muhimmiyar manufa ce ta gwamnatin kasar Sin. Kawo yanzu, Sin ta kafa wani ingantaccen tsarin tabbatar da hakkokin mata, ciki har da zartas da dokoki sama da 100, da kawar da gibin jinsin dake kasancewa a fannin bada ilimi, kuma daga dukkanin mutanen da suka samu ayyukan yi a kasar Sin, sama da kaso 40 bisa dari mata ne. A shekaru biyar da suka shige, shugaba Xi ya yi tayin kaddamar da taron kolin kasa da kasa kan harkokin mata, inda aka bada shawarwarin hadin-gwiwar kasa da kasa a wannan fanni. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da rubanya kokarin tallafawa harkokin mata duk fadin duniya, kana, tana kira da a sake kaddamar da irin wannan taron koli a shekara ta 2025. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

What's On Your Mind?