Shugaba Xi Jinping Da Mahaifiyarsa

- Advertisement -

Shugaba Xi Jinping Da Mahaifiyarsa

Daga  CRI Hausa

A gobe ake bikin ranar mahaifiya bisa al’adun kasashe daban daban, don haka a yau za a gabatar da wani labari da ya shafi wata mahaifiya da danta.

Sunan mahaifiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping, shi ne Qi Xin. Ta zama ‘yar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a lokacin da kasar Sin ke turjewa harin sojojin kasar Japan tsakanin shekarar 1931 da ta 1945. Kana ita ma ta taba zama soja mai yakar maharan Japan. A lokacin tana da shekaru 15 kacal.

Danta Xi Jinping ya dauki mahaifiyarsa a matsayin abin koyi, inda a lokacin da yake da shekaru 15 a duniya, ya tafi kauyen Liangjiahe dake lardin Shaan’xi na kasar Sin, inda ya zauna tare da manoma, da aiki tare da su, har na tsawon shekaru 7, inda ya samu fahimtar yanayin kauyukan kasar Sin. Daga bisani kuma ya shiga jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a can.

Xi Jinping da mahaifiyarsa baki daya, solar kasance ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kokarin bautawa jama’ar kasar. Yin hakan ya zama wani buri nasu na bai daya. (Bello Wang)

 

- Advertisement -