Shugaba Xi Jinping Da Hikimar Sinawa A Fannin Gudanar Da Nagartaccen Mulki

0
83

Shugaba Xi Jinping Da Hikimar Sinawa A Fannin Gudanar Da Nagartaccen Mulki

Daga Bello Wang, 

“Gudanar da nagartaccen mulki” wani babban jigo ne da ‘yan siyasa na kasashe daban daban suke mai da hankali a kai. Shugabanni na kasashen duniya suna kokarin neman dabaru da fasahohi mafi dacewa, don neman samun wata turbar siyasa mai kyau, gami da gudanar da nagartaccen mulki a kasashensu.

A kasar Sin, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kan ragamar mulki, tana kokarin raya tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin irin na zamani, wanda ya sa kasar kawar da talauci a dukkan bangarorinta, da samun ci gaban tattalin arziki cikin matukar sauri. Sai dai a nasa bangare, Xi Jinping, shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, yana kokarin gudanar da ayyukansa masu alaka da mulki, bisa tunanin mulki na zamani, gami da wasu tsoffin tunani masu daraja da aka gado daga kaka da kakani. Dalilin da ya sa Xi yake daukar wannan dabara, shi ne domin kasar Sin wata babbar kasa ce mai dimbin tarihi, inda tsawon lokacin tarihin kasar ya kai shekaru 5000. Kana tun tuni, Sinawa solar kirkiro bakaken Sinanci, inda suka fara rubuta tarihinsu a cikin littafi, don haka ana iya samun dimbin tunani masu daraja recreation da aikin mulki a cikin tsoffin littattafan tarihin kasar Sin. Xi Jinping, wanda ya kasance wani mutum ne dake matukar kishin al’adun kasarsa, ya taba bayyana cewa, “Dole ne a tuna da tarihin wata kasa, daga baya ake iya tabbatar da nagartacciyar makomarta a nan gaba. Dole ne a yi kokarin koyon fasahohi na lokacin baya, daga bisani za a iya kirkiro sabbin dabaru.”

Yau bari mu duba yadda shugaba Xi na kasar Sin yake kokarin gadon nagartaccen tunanin mulki na gargajiya, don taimakawa gudanar da mulki mai kyau a kasar.

 

Aikin mulki ya yi kama da aikin gona

Kamar yadda mutanen Najeriya suke dora muhimmanci sosai kan aikin gona, Sinawa su ma suna kallon aikin gona a wani matsayi mai matukar muhimmanci. Har ma solar taba kwatanta aikin mulki da aikin gona, don samun abubuwa masu kama da juna tsakaninsu.

Gong Sunqiao, shi ne wazirin daular Zheng na kasar Sin, wanda ya rayu tsakanin kimanin shekarar 582 da ta 522 kafin haihuwar Annabi Isa. Ya taba bayyana cewa, “Aikin mulki ya yi kama da aikin gona. Ya kamata a dinga tunanin wasu nagartattun matakan da za a iya dauka, don tabbatar da samun sakamako mai kyau.”

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba tsamo wannan magana, a cikin wani jawabin da ya gabatarwa jami’an gwamnatin kasar, don tunasar musu da su kara kokarin aiki, da sauke nauyin dake wuyansu.

 

Aikin da ya fi muhimmanci a fannin mulki shi ne kwantar da hankalin jama’a

Tun fil azal, har zuwa yanzu, masu kula da mulki na kasar Sin su kan dora muhimmanci sosai kan ingancin zaman rayuwar jama’a. Saboda a ganinsu, moriyar jama’a ita ce tushen wata kasa.

Zhang Juzheng, wani shahararren jami’i ne na kasar Sin, wanda ya rayu tsakanin shekarar 1525 zuwa ta 1582. Ya taba rubuta cewa, “Aikin da ya fi muhimmanci a fannin mulki shi ne kwantar da hankalin jama’a, kana don cimma wannan buri, dole ne a fahimci matsalolin da ke addabar su.”

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba tsamo wannan magana a cikin wani jawabin da ya gabatar, tare da nanata cewa, ya kamata dukkan jami’an gwamnati su sanya burin kyautata zaman rayuwar jama’a a zuciyar su.

 

Dole ne a wadatar da jama’a yayin da ake gudanar da mulki

Don kwantar da hankalin jama’a, dole ne a ba su isashen kudin shiga da suke bukata don gudanar da harkokinsu na zaman yau da kullum.

Guan Zi, wani littafi ne mai bayyana fasahohin mulki, wanda aka wallafa shi tsakanin shekatar 475 da ta 221 kafin haihuwar Annabi Isa, a kasar Sin. An rubuta a cikin littafin cewa, “Dole ne a yi kokarin wadatar da jama’a yayin da ake gudanar da mulki.” A ganin marubucin littafin, idan jama’ar wata kasa solar samu wadatar zaman rayuwa, to, cikin sauki za a iya gudanar da mulki. In ba haka ba, gudanar da mulki zai zama wani aiki mai matukar wuya.

Shugaba Xi Jinping ya taba tsamo wannan magana a cikin wani jawabin da ya yi, inda ya nuna cewa, makasudin daukar matakan raya kasa, shi ne baiwa jama’a alfanu. Saboda haka duk wani irin ci gaban da ake nema a cikin wata kasa, dole ne ya zama mai amfani ga jama’a.

 

Kuskuren wani tamkar husufin rana ne

Duk wani mutum zai iya yin kuskure. Don gudanar da aikin mulki da kyau, dole ne a tabbatar da samun damar gano kuskuren da aka yi, gami da gyara shi cikin sauri.

A cikin wani tsohon littafi mai suna Kalaman Confucius, wanda aka wallafa kimanin shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa a kasar Sin, an rubuta cewa, “Kuskuren da wani mutum mai kirki zai aikata, tamkar husufin rana ko na wata ne. Wato da ya yi kuskure, kowa zai gani. Sa’an nan bayan da ya gyara shi, kowa zai yi masa jinjina da girmamawa.”

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya taba tsamo wannan magana, don bayyana bukatar daidaita kuskuren da ake samu yayin da ake gudanar da harkoki na jam’iyyarsa. Ya ce, wani babban fifikon da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke da shi, shi ne ‘yan jam’iyyar ba su da wata al’ada ta boye kuskure, kana duk wani kuskuren da aka aikata, ana yin iya kokarin neman gano shi, da kuma gyara shi ba tare da wani jinkiri ba.

 

Abubuwa three da ya kamata wani jami’i ya lura

Don gudanar da aikin mulki yadda ake bukata, dole ne a sanya jami’an gwamnati su zama masu bin doka, da masu gaskiya.

Lv Benzhong, wani shahararren jami’i ne kuma mawaki a kasar Sin da ya rayu tsakanin shekarar 1084 da ta 1145. Ya taba rubutawa cewa, “duk wani jami’i, ya kamata ya lura da abubuwa three, wato: Da farko, kar a karbi hanci da rashawa. Na biyu, a yi taka tsan-tsan yayin da ake gudanar da harkokin mulki. Sa’an nan na uku, dole a yi kokarin aiki ba tare da kasala ba.”

Wannan kalami ya yi tasiri sosai a kasar Sin, har ma shugaban kasar Xi Jinping ya taba furta ta a cikin wani jawabinsa don bayyana wasu abubuwan da suka kamata jami’an gwamnati su aikata.

 

Idan an hada karfin mutane da yawa, ko wani abu mai matukar nauyi ma za a iya daga shi

Shugaba Xi Jinping yana dora muhimmanci sosai kan hadin kan jama’a. A ganinsa, dole ne a samu cikakken hadin gwiwar al’umma, wanda zai kai ga daidaita matsaloli daban daban da za a iya fuskanta.

Ge Hong, wani shahararren masanin ilimin hada magani da ya rayu tsakanin shekarar 283 da 363 a kasar Sin. Ya taba rubuta cewa, idan an hada karfin mutane da yawa waje guda, to, za a iya daga abu mai matukar nauyi ba tare da shan wahala ba.

Shugaba Xi ya tsammo wannan magana, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron koli kan batun yanayi na kasa da kasa, wanda ya gudana a ranar 22 ga watan Afrilun da muke ciki. A cewarsa, matsalar muhalli ta sa dukkan halittun dake zama a duniyarmu, ciki har da dan Adam, fuskantar makoma iri daya. Don haka, dole ne mutanen duniya su yi kokarin hadin gwiwa da juna, don neman kyautata muhallin da muke zama a ciki, da daidaita batun dumamar yanayi cikin sauri.

 

Ba za a iya gina gida da katako guda ba

Ban da koyon fasahohin mulki da aka rubuta a cikin tsoffin littattafan kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping shi ma yana kokarin nazarin ilimi da hikima na al’ummomin kasashe daban daban, musamman ma a fannin aikin mulki.

Ya taba tsamo wani karin magana da ke yaduwa a tsakanin wasu kasashen Afirka, wato “Ba za a iya gina gida da katako guda ba.” don bayyana wajibcin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa dake nahiyoyin Asiya da Afirka. Ya ce, a kasar Sin ma akwai wani karin magana da ya yi kama da maganar, wato “Mutum daya baya daukar abu mai nauyi, kana za a fi saukin isa wurin da aka nufa, idan mutane da yawa suka tafi tare.”

Wata muhimmiyar shawarar da shugaban ya gabatar dangane da huldar kasa da kasa, ita ce kafa “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya” a duniyarmu. Karkashin wannan manufa ya kan nemi karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, musamman ma ta la’akari da kyakkyawar huldar da ta dade tana kasancewa tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)

What's On Your Mind?