Shugaba Buhari Yana kokari Amma Makiya Ne Suka Yi Mai Yawa- Gidado

- Advertisement -

Shugaba Buhari Yana kokari Amma Makiya Ne Suka Yi Mai Yawa- Gidado

Daga Idris Aliyu Daudawa

Al’amarin duniya shi dama haka ne yake ba yadda mutum ace yana burge kowa, domin shi din ma tara yake bai cika goma ba, wannan shi yasa ma shi Shugaban kasa Muhammadu Buhari duk wani kokarin da yake yi, da akwai wadanda suke ganin bai tsinana komai ba, wannan haka ne. Idan ma masu karatu  basu manta ko nace bamu manta ba fiyayyen halitta wanda muke koyi da shi a matsayin mu na musulmi,  shi ma bai rasa makiya ba, duk kuwa da darajar da Allah ya yi masa, amma daga karshe ai nasara ta sa ce domin kuwa ai sai da shi addinin musuluncin ya mamaye dukkan duniya.

Alhaji Gidado Idris Bebeji Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal hore na sashen Arewa ta tsakiya, cikin hirra da ya yi da manema labarai a ofishinsa ya nuna bacin ransa da kuma bakin-cikin sa kan irin cin kashin da ake yi wa Fulani wanda kuma ya ce ba a taba yi ba. Ya bada misali da abinda ya faru a Jihar Anambra watan daya gabata, ko kuma 24 ga watan Afrilu inda aka kashe Fulani 19 a Igbariam cikin karamar hukumar Oyi ta Jihar Anambara.Inda ya ce rundunar ‘yansanda ta jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar shi al’amarin.
Ya kara yin bayanin cewa wani abin ban takaici ma sai aka rika tura abin ta kafar sadarwa ta zamani, ana ta turawa, shi kuma aikin kisan Fulani ‘yan kungiyar IPOB ne suka aikata shi, inda suka ce suka samu Fulanin, har muhallin su suka kashe su, ba tare da solar aikata  wani laifin  komai ba. Amma su jami’an tsaro solar ce za su shiga neman wadanda suka aikata mummunar barnar. Amma har yanzu shiru kake ji sai kace an shuka dussa, ko kuma an aiki Bawa garinsu.
Ya yi kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar ya sa a dauki tsattsauran mataki akan kungiyoyi kamar ta ‘yan kabilar Ibo, wadda take cin karenta babu babbaka amma an kasa daukar wani kwakwaran mataki, duk da yake gwamnatin tarayya, kamar yadda ya ce ta soke ta amma sokewar bai hanata ci gaba da aikata miyagun ayyuka ba.
Bugu da kari kuma ita ma kungiyar tsaro ta sashen Kudu maso yamma da ake kira da suna Amotekun ita ma tana gallazawa ‘yan kabilar Fulani, don haka ita ma ya dace a taka mata burki, akan wasu abubuwan da take aikatawa. Abin nata idan aka duba sosai ai za a gane  baya ma ga tsaron da ake cewa tana yi na sashen da suke, ai duk da hakan suna aikata assha.
Har ila yau ya ce bai kamata ace kullun sai dai a sa ido ana ganin suna aikata ayyukan assha wadanda basu dace ba, amma kamar solar fi karfin aja masu kunne ne.
Ya kara jaddada cewa “Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yin iyakar kokarinsa wajen aiwatar da ayyukan ci gaban kasa, sai dai kuma yana da makiya masu matukar wuya, wadanda su duk wani kokarin da  yake yi, solar san yadda za su bata abin”.
kungiyoyi na Fulani kamar yadda ya yi karin bayani irin su Miyetti Allah, da Miyetti Allah Kautal Hore su ba, kungiyoyin da suka damu da tashin hankal nei ba, sai dai idan an saba masu su kai al’amari a kotu, inda suna sa ran za a bi masu hakkin  su kamar yadda ya dace.

- Advertisement -