Shugaba Buhari Ya Yaba Wa Sarkin Kano Bisa Kyautata Alaka Da Sauran Masarautu – Ganduje

- Advertisement -

Shugaba Buhari Ya Yaba Wa Sarkin Kano Bisa Kyautata Alaka Da Sauran Masarautu – Ganduje

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Shugaban kasa Muhannadu Buhari ya jinjinawa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero bisa gina kyakkyawar alaka da sauran masarautun kasarnan shugaban kasar na alfahari da wannan kokari.

Wannan jawabi na kunshe cikin jawabin da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar a lokacin hawan Nasarawa, cikin bukukuwan Sallah karama lokacin da sarkin ya kai ziyarar gaisuwar Sallah fadar Gwamnatin ranar Asabar da ta gabata.

“Ina matukar farin cikin sanar da ku cewa lokacin da kuke zagayen ziyartar sarakuna a kasar nan, Shugaban kasa Muhannadu Buhari ya yi farin ciki da hakan,” In ji shi.

Ya kara da cewa, ita kanta Gwamnatin Tarayya ta yi farin ciki da kyakkyawar alaka da sauran Masarautu a fadin kasa baki daya. Saboda haka babwai Jihar Kano kadai ba ke farin ciki da wannan kyakkyawar dabi’a ta sarkin ba har ma da daukacin al’ummar Nijeriya.

“Shugaban kasa ya yimin waya inda yake bayyana min gamsuwarsa bisa kokarin da kake wajen kyautata alaka a fadin kasar nan. Ina nufin ziyarar da sarkin ke kai wa sauran sarakunan kasar nan. Haka sarakuna da yawa suka kira ni suna bayyana farin cikinsu kan wannan kokari da kake yi.

Daga nan sai Gwamna Ganduje ya jadadda cewa za’a ci gaba da mutunta juna tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da masarautun Kano.

Haka zalika gwamnan ya tunatar da cewa Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya zauna lafiya da Gwamnatin Jihar Kano. “Zuwanka a yau sai ya tuna min marigayi sarkin na Kano, wanda muka zauna tare kuma muka yi aiki cikin kwanciyar hankali.

Da yake tsokaci kan batun filin idin dake kofar mata, wanda wani bangare na Jama’a ke korafi kan matakin masarautar na gina kantuna da suka zagaye filin idin, gwamnan ya tabbatarwa da masarautar cewa an cika dukkan ka’idojin gina kantunan.

“Ina wadanda ke cewa masarautar ba ta yi daidai ba, lokacin da aka yanke shawarar gina kantunan a zagayen filin Idin tare da aiwatar da aikin, Suje Masallacin Harami Dake Makka da Madina su ga yadda masallatan biyu ke zagaye da kantuna.

Daga nan sai ya fayyace cewa, ” Masarautar ta bi dukkan matakan da suka dace kafin aiwatar da aikin gina kantunan. Duk wanda ke fadin cewa masarautar ba ta bi ka’i’da ba, wannan soki burutsu ne kawai domin an cika dukkan ka’idojin kamar yadda aka tanada.”

Kamar yadda Gwamnan ya yi wa sarkin bayanin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, gwamna ya bayyana samar da tashar jirgin kasa da za’a kammala aikinta zuwa karshen wannan shekara. Wanda ya ce, fatanmu shi ne a saukaka harkokin kasuwanci domin ‘yan kasuwa dinga samun kayansu daga kasashen waje, ba tare da bi ta tashar jiragen ruwa dake Legas ko Fatakwal ba. Hakan zai habaka tattalin arzikin mu,”

Shi ma da yake gabatar da jawabinsa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da aniyar masarautar da sauran Masarautun Kano guda hudu ci gaba da goyon bayan tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kano domin tabbatar da cigaban Jihar.

“Muna matukar godiya ga Mai Girma Gwamna bisa kokarin sake maido da kimar Jihar Kano, ko shakka Babu hakan abin a yaba ne kwarai da gaske. A wannan wuri nake son bayyana cewa, a madadin sauran sarakunan Jihar Kano, mun yi alkawarin ci gaba da goyon bayan kyawawan manufofi da tsare-tsaren gwamnati.” In ji Sarkin.

Sarkin ya bukaci al’umma da ako da yaushe su ci gaba da neman gafarar ubangiji, domin Jihar Kano ta ci gaba amfana da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da dorewar cigaba.

“Dukkanin mu muna jinjina wa kokarin Gwamnatin Jihar Kano bisa Inganta harkar tsaro a jihar, wannan babu shakka abin a yaba ne kwarai da gaske,” in ji shi. Kamar yadda babban Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya shaida wa MOBILIZED9JA A Yau.

- Advertisement -