Shugaba Buhari Ya Dawo Daga Kasar Faransa

- Advertisement -

Shugaba Buhari Ya Dawo Daga Kasar Faransa

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga birnin Paris na kasar Faransa, bayan ziyarar kwanaki hudu da ya kai domin halartar taron habaka sha’anin kudi na kasashen Afirka.

Mai ba Shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da wannan a jiya Alhamis a shafinsa na twitter.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan nasarar taron sha’anin kudi na kasashen Afirka wanda ya mayar da hankali kan nazarin tattalin arzikin Afirka, biyo bayan rikicin da annobar Korona ta haifar,” a sakon tare da hotunan isowar Buhari.

A yayin ziyarar, Shugaba Buhari da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron solar sadaukar da kasashensu biyu don yin aiki tare don yaki da rashin tsaro da ke addabar yankin tafkin Chadi da dukkan yankin Sahel.

Shugaba Macron na Faransa ya yi alkawarin ba da goyon baya dari-bisa-dari ga Nijeriya da jama’arta yayin da suke fuskantar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Macron ya yi wannan maganar ne a ranar Talatar da ta gabata a wani taron bangarorin biyu, wanda ya karbi bakuncin Shugaba Buhari a gefen taron kasafin kudin Afirka a Paris.

Ya ce, gwamnatin Faransa za ta kasance gaba daya a gefen Nijeriya, kuma a shirye take ta ba da goyon baya da komai don taimakawa kasar don shawo kan barazanar tsaro. Ya kuma yi alkawarin tallafawa Nijeriya wajen tunkarar kalubalen da aka fuskanta sport da allurar riga-kafin Korona.

Shugaba Buhari, yayin da yake jawabi a wurin taron kasafin kudi na Afirka wanda aka gudanar a Grande Palais Ephemere tare da taken ‘Kula da harkokin waje da kuma biyan bashi’, ya yi kira ga kasashen Turai da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da su yi la’akari da rage tasirin cutar ta Korona kan tattalin arzikin Afirka ta hanyar sake fasalin bashin manyan fayiloli da neman cikakken taimako.

Shugaban ya kara da cew, ya kamata kuma a rage tasirin cutar ta hanyar sakin allurar riga-kafi zuwa nahiyar, wanda har yanzu ke kare galibin ‘yan kasar.

A ranar Laraba a Paris, lokacin da yake ganawa da Shugaban kamfanin Whole, Patrick Pouyanne, Mataimakin Shugaban, AirBus, Silbere Delaunay, Shugaban kwamitin wani kamfanin software program, Daussault Methods, Florence berzelen, Shugaban Injiniyoyi da Shugaban kamfanin sadarwa na kamfanin sadarwa, Francois-Regis Teze da Shugaban kamfanin Donafled Automotibe, Dakta Donatus Nwokoye, wani hamshakin kamfanin da ya yi nasara.

Shugaba Buhari ya yi kira ga masu zuba jari da su kara zurfafa damammaki na mutane da albarkatun kasa a Nijeriya.
Ya tabbatar wa da masu zuba jarin cewa manufofin kasafin kudi za su kasance masu matukar amfani, wanda za a iya hangowa kuma a tafiyar ta yadda za a samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci.

- Advertisement -