Shugaba Buhari ya Bada Umurnin Daukar Ma’aikatan N-Power zuwa Mutum 1, 000, 000 Maimakon 500,000

0
106

Shugaba Buhari ya Bada Umurnin Daukar Ma’aikatan N-Power zuwa Mutum 1, 000, 000 Maimakon 500,000

A kokarin shugaba Muhammad Buhari na fitar da mutanen Najeriya miliyan 100 daga talauci, an kara adadin wadanda za su amfana da shirin gwamnatin nan.

Nan da shekaru 10 masu zuwa, shugaban Najeriyar ya ci burin raba miliyoyi daga kangin talauci.

Jaridar The Nation ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya fadada aikin gwamnatinsa ta hanyar kara yawan wadanda za su amfana da tsarin matasa na N-Power.

Majiyarmu ta dauko daga jaridar Legit Shugaban kasar ya bada umarni a kara yawan Bayin Allah da ke cin moriya da manufofin da gwamnatin APC ta kawo domin kawar da radadin talauci a kasa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bada umarni ne ga ma’akikatar bada agaji da jin-kai na kasa, ta kara yawan ma’aikatan N-Power daga 500,000 zuwa 1,000,000.

Gaskiya Yakamata Buhari Yaji Wannan. Malamai Sun Fara Fusata Suma Sakon Manoma 110 Da Anka kashe

Shugaban Najeriyar ya kuma umarci ma’aikatar cewa ta dada yawan wadanda zasu ci moriyar tsarin GEEP da gwamnatinsa ta kawo da mutane 1, 000, 000.

Ba a nan kawai shugaba Muhammadu Buhari ta tsaya ba, ya nemi a kara mutane 500, 000 a cikin yaran da ake ciyar wa a kananan makarantun gwamnati a kasar.

Minista Sadiya Farouq ta bada wannan sanarwa a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da ita domin ta bayyana irin nasarorin da ta samu a shekara daya da ta yi a ofis.

Farouq ta ce gwamnatinsu ta yi duk wannan ne domin karfafa matasa. Ana sa ran wannan makudan kudi da ake batar wa za su farfado da tattalin Najeriya.

What's On Your Mind?