Shugaba Buhari Ga Sufeton Yan Sanda: Ka Gaggauta Duba Matsalolin Da Yasa Jama’a Ke Kuka Da SARS

0
63

Shugaban Muhammadu Buhari  ya umarci shugaban rundunar yan sanda na kasa Mohammed Adamu ya gaggauta duba matsalolin da ake kuka akai da yadda jami’an yan sanda na farin kaya da akafi sani da SARS ke gudanar ayyukan su.

Buhari ya sanar da hakan ne a ganawar da ya yi da Mohammed Adamu a fadar shugaban kasa dake a Abuja, inda ya kuma ya umarce shi da ya gaggauta magance korafin da yan Nijeriya ke yi da kira da a rushe rundunar tsaro na SARS.

A cewarsa, ya sake ganawa da Sufeto Adamu cikin daren juma’ar data gabata kuma ya umarce shi ya gaggauta duba matsalolin da ake kuka akai da yadda jami’an SARS din ke gudanar ayyukan su.

Ya kara da cewa, yana sane da irin sauye sauyen da ake yi a rundunar Yansanda, amma bai dace ace kuma maimakon agyara sai arika kukan batawa ake yi ba.

Shugaba Buhari Ga Sufeton Yan Sanda:  Ka Gaggauta Duba Matsalolin Da Yasa Jama’a Ke Kuka Da SARS

Buhari ya kara da cewa,  ya umarce shi da kakkausar murya cewa lallai ya bi diddigin korafe-korafen da yan Nijeriya keyi akan ayyukan SARS din domin magance su sannan wadanda suka aikata ba daidai ba ya tabbata an hukunta su cikin gaggawa.

Ya kuma roki yan Nijeriya su cigaba da hakuri su duk da ko suna da daman nuna rashin amincewarsu ga yadda jami’an ke muzguna wa mutane, cewa lallai za a gyara.

NANS Ta  Kasa Ta Karrama Hajiya Aisha Maikurata A Kebbi

An kafa SARS domin dakile manya ko muggan laifuka da su ka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran mugayen mutanen da ke hana al’umma zaman lafiya.

Sannu a hankali sai wasun su aka rika amfani da su wajen gallazawa, azabtarwa ko kuma koya wa wani ko wasu hankali’ta hanyar da shari’ar tsarin dokar kasa bai tanadar ba.

What's On Your Mind?