Shirya Kowane Irin Taron Kasa A Yanzu Ba Shi Da Alfanu –Tanko Yakasai

- Advertisement -

Shirya Kowane Irin Taron Kasa A Yanzu Ba Shi Da Alfanu –Tanko Yakasai

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Kamar yadda kowa ya sani ne, babu wata doka a cikin kundin tsarin mulki da ta bai wa wata kungiya a Nijeriya shirya wani taro da sunan taron kasa, don haka babu alfanun kiran irin wannan taron a irin wannan lokaci da ake ciki.

Jawabin haka ya fito ne daga bakin guda cikin jajirtattun dattijan kasa, Alhaji Tanko Yakasai a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan soki burutsun da wasu ke yi na lallai sai a kira taron kasa domin baje komai a kan faranti.

Alhaji Tanko Yakasai ya ce idan ana bukatar yin hakan dole sai dai Majalisun kasa su samar da wata doka da za ta bayar da irin wannan damar gudanar da taron kasar ga Shugaban kasa, Majalisar Dattijai ko Sashin Shari’a domin shirya irin wannan taron kasar.

Ya kara da cewa irin wannan karfin iko bai hada da bai wa kowacce hukuma damar samar da wani canji a kundin tsarin mulkin kasa ba. Sauran tarukan kasar da aka yi yunkurin gudanarwa a lokacin mulkin soja wanda solar yi amfani da karfin ikon da suke da shi ne wanda ya ba su damar shirya irin wannan taron tare da kokarin aiwatar matakan da aka dauka.

To, Yanzu kuma muna cikin mulkin Dimukuradiyya wanda yake  da hukumomi da aka zaba a siyasance domin jan rakamar ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya basu.

“A iya sanina lokuta uku aka gudanar da tarukan kasa a Nijeriya, biyu daga ciki a lokacin mulkin soja na zamanin Janar Murtala/Obasanjo sai kuma a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Sauran biyun da akayi kokarin gudanarwa su ne lokacin Obasanjo da Goodluck. Daga nan sai suka zama shawara ce kawai, yayin da aka yi watsi da sauran ana tsaka da aikinsu sakamakon rashin ingantacciyar kariyar shari’a.” In ji shi.

Yace baya ga haka ma yanzu muna da sauran kasa da Shekara biyu na wannan Gwamnatin ta kare, idan haka ne kuwa ashe bamu da isasshen lokacin gudanar da wannan taron. Domin babu lokacin zabar wakilai a kowane irin taron kasa, balle batun dokar da za’a aiwatar da taron akanta.

Sannan kuma ga dandazon kungiyoyin gangan a kasarnan irinsu kungiyar tsagerun Yarabawa ta Afenifere, masu rajin IPOB, Oduduwa da sauran su da a halin yanzu Gwamnati ta haramta su a Nijeriya baki daya.

Idan aka dubi kunshin Majalisun kasa kowane bangare nada wakilci, walau a Majalisar dokokin Jiha ko matakin kasa. Zamu iya amfani dasu wajen gabatar da kowace irin shawara da muke da ita ga zababbun namu a wadancan Majalisu domin magance dukkan matsalolin da muke dasu.

Kasancewar akwai wadancan  hukumomi a kunshin Kundin tsarin Mulkin kasa, zasu iya jagorantar taron kasa idan muna da wadataccen lokacin gudanar da taron wadda za’a kada kuri’ar rashin amincewar wakilanmu a matakan kasa da jihohi.

A karshe ya ce lallai akwai bukatar a yiwa irin wannan bukatar ta wasu da ke fatan samun kowace irin dama domin wargaza kasar baki daya kallon tsanaki.

 

 

- Advertisement -