Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Zama Babban Dandalin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa

0
69

Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Zama Babban Dandalin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa

Daga CRI Hausa

 

A yau Talata kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, a halin yanzu, shirin “Ziri daya da hanya daya” yana kasancewa babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, wanda ya hada kan sassa daban daban, wajen neman makoma mai haske.
Bisa kididdigar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fidda, cikin rubu’i na farko na bana, jarin da aka zuba kai tsaye, wanda bai shafi sha’anin kudi ba, cikin kasashe masu alaka da shirin, ya karu da kaso 5.2%.
Wang Wenbin ya ce, kwanan baya, kasashen Sin da Botswana da Congo(Kinshasa) solar kulla yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shirin “ziri daya da hanya daya”. Kaza lika ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 200 da kasashe 140, da kungiyoyi guda 31.
Har ila yau, bisa ci gaban shirin “ziri daya da hanya daya”, ana aiwatar da shirye-shirye da dama, wadanda suka karfafa mu’amalar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen da abin ya shafa, yayin da kuma ake samar da ayyukan yi da dama ga mutane masu yawa. Lamarin dai ya karfafa bunkasuwar tattalin arzikin wurin, da kuma inganta rayuwar al’umma na wuraren. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

What's On Your Mind?