Shirin Rage Talauci A Nijeriya Zai Kankama Yayin Da Aka Amince Da Shi

0
148

Shirin Rage Talauci A Nijeriya Zai Kankama Yayin Da Aka Amince Da Shi

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Shirin Rage Talauci na Kasa da Matakan Bunkasa Ci Gaba wanda Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bayar da sahihan shawarwari a kan tattalin arziki ya gabatar.

Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo shi ne zai jagoranci kwamitin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labaru, Femi Adesina ya sanar da haka a ranar Laraba sa’ilin da yake yi wa manema labaru na fadar gwamnati jawabi a karshen taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya karo na 43 da ya gudana ta hoton bidiyo, bisa jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Adesina ya yi bayanin cewa, bugu da kari, majalisar ta kuma amince da aiwatar da shirin na rage talauci da habaka shi zuwa cikin tsarin bunkasa kasa mai matsakaicin zango da za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa 2025 da kuma babban kudirin nan na cimma ci gaban kasa a shekarar 2050.

Ya kuma ce majalisar ta umurci Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Kasa Abubakar Malami ya tsara kudirin doka kan wadannan matakai domin aike wa Majalisun Dokoki na Kasa saboda a samu sukunin dorewar aiwatar da shirin.

Ya kara da cewa, majalisar ta kuma yi la’akari da irin damuwar da talauci ya haifar a kasar nan a sa’ilin da ake tafka muhawara a kan shirin na rage radadin talauci.

Gwamnati mai ci dai ta sha bullo da matakai da tsare-tsare daban-daban na kawar da talauci a Nijeriya, inda wasu shirye-shiryen suka tabuka, wasu kuma sai dai a ce “”uhum”, in ji mai ciwon hakori.

What's On Your Mind?