Jarumi Lawal Ahmad – Shirin ‘Izzar So’ Ya Zama Garkuwa Ga Mutuncin Masana’antar Kannywood

0
152

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da Lawal Ahmad, JARUMI KUMA MAI SHIRYA FINA-FINAI A MASANA’ANTAR FINA-FINAI TA KANNYWOOD, WANDA YA SHIRYA FITACCEN SHIRIN NAN MAI SUNA IZZAR SO.

To Da Farko Dai Za Mu So Ka Fada Mana Cikakken Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.

To Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarkatuh. Sunana Lawal Ahmad, kamar yadda kowa ya sani. Kuma ni mutumin Katsina ne, an haife ni a garin Bakori a Unguwar Tofa. Na yi makarantar Firamare a nan Nadabo Firamare da ke Bakori. Na yi Sakandire a Gobernment Secondary School Bakori zuwa aji uku. Daga nan na taho Kano na ci-gaba a Sakandire ta Sharada daga aji hudu zuwa aji shida. Bayan na gama kuma sai na tafi Federal College Of Education ta nan Kano, na yi Diploma a Public Admin. To bayan nan ne na fara harkar fina-finai.

Shirin ‘Izzar So’ Ya Zama Garkuwa Ga Mutuncin Masana’antar Kannywood

To Me Ne Ne Ya Ja Ra’ayinka Har Ka Shiga Wannan Harka Ta Fina-finai?

To a kodayaushe a ka yi min wannan tambayar ina cewa ni gaskiya sha’awar harkar fim din ce ta kawo ni. Kawai ni na ga a na yi ne sai ni ma na ji ina da sha’awar na ringa yi. Sai da na shigo na ga ashe harka ce ma da za ka ringa samun na kaiwa baki, ka na rufawa kanka asiri, ka na yin sutura da sauransu. To sai na kara rike abun sosai, wannan shi ne dalili.

Kusan Duk Wani Jarumi Ko Jaruma Ya Kan Samu Tsanin Da Ya Hau Kafun Shigowa Wannan Masana’anta Ta Fina-finai, Wa Ne Ne Tsanin Jarumi Lawal Ahmad?

To gaskiya farkon shigowa ta ba ni da wani tsani, amma bayan na shigo sai Allah Ya sa mu ka hadu da su marigayi Ahmad S. Nuhu, su Sadik Mafia, mu ka fara zama da su mu na dan zuwa wajen su su na dan bamu shawara a kan abun. To daga nan sai mu ka hadu da su Ali Nuhu ta hanyar su Sadik Mafia din da  kuma marigayi Ahmad S. Nuhu Allah Ya jikan shi. To a nan ne mu ka fara aiki da kamfanin shi Ali Nuhu wato FKD, to a nan mu ka zauna mu ka ci-gaba da aiki, har kuma zuwa yanzu da Allah Ya kawo matsayin da mu ke yanzu.

Ka Na Da Wata Alaka Ta Jini Ne Da Su Jarumi Ali Nuhu Da Marigayi Ahmad S Nuhu?

To gaskiya ba mu da alaka ta jini da su. Sai dai rayuwa ce ta hada mu. Kuma kasan duk mutumin da ya ke so ya yi karko ko ya samu abunda ya ke so, to dole fa sai ya yi biyayya. Ba abunda ya sa a ke ganin kamar uwarmu daya ubanmu daya da su sai biyayya. Mu na biyayya ga abubuwan da su ke saka mu saboda mun san ba za su cutar da mu ba. Haka kuma abunda su ka ce mu bari mu na bari, to wannan ne ya sa a ke ganin kamar mu na da alaka ta jini. Amma dai gaskiya mun zama ‘yan uwa sosai ta dalilin wannan harka ta fim.

Jarumai Da Yawa Su Kan Fuskanci Kalubale Da Yawa Idan Su Ka Bayyana Niyyarsu Ta Shigowa Harkar Fim, Kai Ma Ka Samu Irin Wannan Kalubalen?

Aa ni gaskiya ban fuskanci wani kalubale ba. Saboda ni Malam Ahmad Ibrahim Sulaiman wanda kowa ya san alakarmu da shi, kanin mahaifiyata ne kuma shi ya kawo ni Kano, a wajensa na zauna na yi karatu na boko da na Arabiyya. Lokacin da na fada masa ya jajja kunnena dai a kan cewa in kiyaye addinina, in kiyaye nasabar gidan da na fito da sauransu. To wannan dai shi ne, amma ni ba wanda ya hana ni ko yace kar in yi fim ko a na kyamatarsa ko wani abu. Gaskiya ni ba wanda ya hana ni.

Wanne Ne Fim dinka Na Farko A Cikin Wannan Masana’anta?

Fim dina na farko a cikin wannan masana’anta shi ne “Izina” wanda Sadik Mafia ya bayar da umarninsa. Amma fitowa daya na yi a cikinsa. Kafun fim din kuma ya fita kasuwa sai mu ka yi wani fim mai suna “Siradi” wanda Jamilu Kazaure ya bada umarni, wanda shi kuma na fito ne a kanin Ahmad S Nuhu, na fito da suna Bello. To a nan ne dai na fara fitowa a matsayin cikakken jarumi. Daga nan kuma sai na yi fim din “Zuma” na kamfanin FKD. Inda Ali Nuhu ya saka ni a fim din Zuma inda mu ka yi tare da Maijidda Ibrahim. Daga nan kuma sai mu ka ci-gaba da harkokinmu.

To Ya Ya Ka Samu Kanka A Cikin Wannan Shiri Na Siradi Duba Da Cewa Shi Ne Fim Dinka Na Farko?

To Alhamdulillah tunda daman mu na kaunar abun, kuma Allah Ya hada mu da kamar su shi Jamilu Kazauren, Mafiyan da su marigayi Ahmad S Nuhu duk abunda mu ka yi ba dai-dai ba za su ce mu gyara nan da chan sai kuma mu gyara. Idan kuma mun yi dai-dai za su kara mana karfin gwiwa.

To Daga Lokacin Da Ka Fara Fim Zuwa Yanzu Za Ka Iya Fada Mana Adadin Fina-finanka?

Gaskiya ba za su irgu ba wallahi, da dai na so na fara irgawa to amma sai abubuwan su ka yi yawa sai na daina. Amma dai suna da yawa gaskiya.

Bidiyo: Jami’an SARS sun bindige wani Yaro Karami, sun tuka Motar sa kirar Lexus Jeep a jihar Ughelli Delta

Wanne Fim Ka Fi So A Cikin Fina-finan Da Ka Yi?

To ni dai gaskiya duk fim din da na yi ina kaunar sa. Sai dai akwai kamar su Taraliya, su Sharhi, Sai watarana, irinsu Kolo, Ba ni ba ke, sai kuma shakundum mai lokaci yanzu wato “Izzar So” tunda shi ya zama zakaran gwajin dafi a yanzu, saboda duniya ta na kallon shi sosai yanzu. To shi ma ya na daga cikin Fina-finan da na ke so gaskiya.

To Mu Dawo Cikin Shirinku Na Izzar So, A Matsayinka Na Wanda Ya Shirya Wannan Shiri wato Furodusa, Me Ne Ne Ya Jawo Hankalinka Ka Shirya Shirin Izzar So?

To Alhamdulillah ka san idan mutum ya na so ya yi wani abu sabo ko kuma wanda duniya za ta kalla, da farko dai ina so in ce mu ku “Izzar So” ikon Allah ne. Don ko lokacin da mu ka fara shi ba mu san zai karbu haka ba. To amma lokacin da mu ka fara shi mu na yi-mu na yi, sai mu ka ga cewa fim din ya dakko labarin da zai shiga jikin al’umma kai tsaye, shiyasa sai mu ka kara tsayawa mu ka Inganta shi, mu ka kara masa kima, mu ka kara masa daraja domin nuna karfin addinin musulunci, karfin tarbiya, karfin tsare gaskiya, a nuna gaskiya gaskiya ce kuma karya karya ce, to sai mu ka kara rike shi a kan wannan layin ta yarda zai isarwa al’umma sako kai tsaye. Kuma Alhamdulillahi an samu abunda a ke so, saboda al’umma photo voltaic karbe shi.

Me Ya Sa Wannan Shiri Naku Na Izzar So Ya Zo Da Tsari Na Dogon Zango, Ba Kamar Yadda Ku Ka Saba Yin Fina-finanku ba?

Eh to gaskiya a duniya ma yanzu, idan ka duba Indiya ko America za ka ga duk irin wannan Fina-finan su ke masu dogon Zango. Su kan saka addininsu da al’adarsu a ciki, da kuma abubuwan da za su saka a dade a na kalla ba tare da an gaji ba. Shiyasa mu ma mu ka gwada kuma Alhamdulillah mu na samun nasara.

Zamu ci gaba a mako mai zuwa.

What's On Your Mind?