Bincike – Shirin Anchor Borrower Na Cigaba Da Fuskantar Matsala

0
35

Shirin Anchor Borrower Na Cigaba Da Fuskantar Matsala

Tun lokacin da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tad are karagar mulkin kasar nan a shekarra 2015, take ta yin kokari wajen farfado da fannin aikin noma ta hanyar samar da tsare-tsare da kuma shirye-shirye, musamman a fanin noma shinkafa.

Wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka shine, na hana shigo da shinkafar cikin kasar nan daga kasashen waje bisa nufin karawa manoman ta kwarin gwaiwa da kuma inganta sana’ar tasu.

Shirin Anchor Borrower Na Cigaba Da Fuskantar Matsala

Hakan ne ya sanya a cikin watan Nuwamban shekarar, Shugaba Buhari ya shugabanci kaddamar da wani gagarumin shirin noman shinkafa na kasa baki daya na Anchor Borrower a Jihar Kebbi.

Har ila yau, a karkashin shirin Anchor Borrower, inda manoman shinkafar kasar nan ake basu bashin kayayyakin aikin noman shinkafa da kiyasinsu ya kama daga naira dubu 160, zuwa naira dubu 217, a kan kowace kadada guda.
Ana dai bayar da bashin nne gwargwadon yawan kadadar da manomi zai noma ana kuma bukatar manomin ya biya daga shinkafar da ya noma.

Shirin na Anchor Borrower, wanda karkashin Babban Bankin Nijeriya ake gudanar da shi da farko gwamnatocin jihohi suka rika daukar wa manomansu lamuninsa.

kungiyar manoman Shinkafa ta kasa RIFAN, a karkashin rassanta na jihohi da Abuja ta maye gurbin gwamnatocin jihohi wajen tsaya wa mambobinsu a kan lamunin.

A yanzu haka dai, bashin da Babban Bankin ya bayar ga yayan kungiyar ta RIFAN ya kai naira tiriliyan daya da biliyan daya kuma ana ci gaba da bayarwa, don kuwa na samu labari a yanzu haka shirye-shirye photo voltaic yi nisa daga Babban Bankin wajen raba bashin noman shinkafar ranin bana ga yayan kungiyar ta RIFAN duk da taurin bashin da wadansu suke da shi.

Shirin noman shinkafar ya sanya a watan Agustan bara, Gwamnatin Tarayya ta rufe iyakokin kasar nan kuma daya daga cikin dalilan yin hakan da ta bayar har da tabbatar da kudirinta na tunda ta fara shirin inganta noman shinkafar na cewa kwaya daya ta shinkafar ba ta kara shigowa ba cikin kasar nan daga kasashen waje ba.

KU KARANTA: Za Mu Cigaba Da Gudanar Da Taron Bajekolin Noman Albasa

Amma abin taiakci, wasu manoman da suka amfana da bashin a karakashin shirin sunki biya.

Bugu da kari, an dauki matakan matsin lamba a kan gwamnatocin jihohi da shugabannin kungiyar RIFAN da Babban Banki ya fara, ya sanya gwamnatocin jihohi ta karkashin shugabannin rassan jihohi na kungiyar RIFAN photo voltaic fara daukar matakan ganin ta kowane hali manoman shinkafar masu taurin bashin photo voltaic biya bashin.

Kamar a Jihar Kano, manoman shinkafa sama da dubu 200 suka amfana da bashin naira biliyan 100 tun da aka fara shirin a shekarar 2017, kuma da kyar da jibin goshi zuwa yanzu manoman suka biya naira biliyan daya da miliyan 200.

A jihar Kebbi kuwa inda shugaba Buhari ya fara kaddamar da shirin a shekarar 2015, Shugaban kungiyar RIFAN reshen jihar, Alhaji Muhammad Sahabi, manema labarai suka ruwaito yana cewa duk da irin alherin da manoman shinkafa a jihar suke samu tunda aka bullo da shirin, amma yanzu maganar da ake yi, manoman shinkafa dubu 70 da suka amfana da shirin, inda kuma suka ki biyan bashin da aka basu.

What's On Your Mind?