Shin Shigar Banxa Ke Janyo Yin Fayde….?? Ku Karanta Cikakken Dalili

- Advertisement -


Na yi matukar bukatar a tauna lamarin fyade ba tare da kallon sa a bangarance ba, amma tataburzar da ake samu tsakanin masu kallon shigar banza a matsayin dalili ko rashinsa ya hana wannan bukata tasiri. 

Duk da haka ba zai hana matsalar zama matsalar al’umma wadda ake bukatar saninta da musabbabinta da maganinta ba maimakon matsalar da wasu ke zaton abar nazari ce da mujadalar kafofin sada zumunta zalla.

Fyade dai laifi ne babba wanda ke karbar hukumce-hukumce da dama a addinin Allah ko a hukumance. Ciki akwai hukumcin Zina, hukumcin cin zarafi, hukumcin amfani da karfi, hukumcin yada fasadi, hukumcin cutar da wani ba da son sa ba. 

Fyade ba abu ne da ya takaita ga haike wa mata ba, har maza ana yi wa, sannan babu wata kasa ko wani yanki da ya kubuta daga sharrin fyade, don haka babu yadda za a yi ya zamo abu mai dalili daya ko dalili iri daya, ko dalili fuska daya ko dalilin hange daya. Dole akwai dalilai masu yawa wasu na kusa wasu na nesa.

Idan zamu kalli shigar banza tare da fyade ta fuskar hukumci, zany ga Fyade a wani rukuni  na Zina a musulunci, yayinda shigar banza ke rukunin ababen janyo sha’awa ga Jima’I kowane iri Zina, ko fyade ko sunnah, kamar yadda rashin iya dauke idon maza da ga kan mata ke  zama husainin wannan rukuni na janyo sha’awa hakan ta sanya Allah SubhanaHu wataala Ya yi kira da anisance wadannan tagwayen halaye a lokaci guda, wato ya umarci mata su yi sutura, su kuma maza su dauke ido, kenan idan za a bi umarnin Allah to dole mata su yi Sutura, kuma idan ba su yi ba da za a bi umarnin Allah cewa maza su sunkuyar da idanunsu kenan ba zasu ga me shigar banza da tayi wa Allah taurin kai ba. Kenan bijirewar Me daga ido ya kalli me shigar banza da ita kanta shigar banzar laifuka ne na 50/50 wanda idan aka kara da na fyade sai mai fyaden ya kwashi 80%

Babban abin takaici shine Fyaden da ya fi daukan hankali shine irin wadanda ake wa yara kanana da ba su dauke da duk wani kayan janyo sha’awa mazansu da matansu ballantana hukumcin shigar banza ya rataya akansu. Kuma ga masu bibiyar alkaluman fyade na gaske ba don kawai su kare laifin fyade da uziri ba, za su fahimci cewa alkaluman yi wa yara fyade anan ketarenmu ya fi na yi wa manyan mata masu kayan kwalliyarmace, shin su ma yaran mummunar shiga suke yi ko kuwa yara maza da ake yiwa fyade na cikin rukunin wadanda aka ce su ja hijabinsu zuwa kasa? 

Watakil amsar ta iya zama cewa wasu matan ne suka yi mummunar shiga ta taso da sha’awar me fyaden da ya zo ya kare a kan yara. Amma me ya sanya bai haye wa masu mummunar shiga ba sai yarinyar da bata kai wannan minzalin ba? 

Arewa ta ciri tuta a kan lamarin fyade a wannan lokacin, musamman Arewar da tun a shekara ta 2000 wato shekaru ashirin cif kenan da kaddamar da Shari’ar musuluncinta Kashi 90% na mata suka rungumi Hijabi a matsayin kayan sanyawa fiye da matan da masu zani da riga da mayafin atamfa da ba su yi fama da fyade a zamaninsu ba sai a zamanin Hijabi. Kenan Hijabi na cikin dalilan ta’azzarar fyade a Arewa ko shi ma mummunar shiga ne?

Mai biye da alkaluman wadanda ake wa fyade zai fahimci cewa matan da ake kuka da su wajen shigar banza ba su samar da kashi 25% a cikin matan da ake wa fyade a Arewa ba, yayinda mata masu sutura suke da fiye da kashi 47% ba.

Alkaluman fyade na nuna cewa kashi 70 daga wadanda ake wa fyade yaran talakawa ne da basu da kudin kayan kwalliyar jan hankalin mazansu ma balle mazan waje sanadiyyar neman na sanyawa a bakin salati. Shi wannan ma mummunar shiga ce?

Mazajen da ke aiki a birane wadanda su ke taammuli da mata masu shigar banza a kulli yaumin su ne ke da karancin adadin masu yin fyade idan aka kwatanta da alkaluman fyaden da mazajen da basa hulda da irin wannan mata ke yi.( idan akwai Dansanda mai izinin sanya baki a wannan sashin ya agaza da bayani don ban da cikakken izini) shi kuma wannan me zamu kira shi?

Tarihin bahaushe wanda aka san matarsa daurin kirji babu isasshen sutura ko rigar Fulani da bata wuce mazaunin Bireziya ba ga mace saboda rashin isasshen sutura duk da haka tarihin bai ruwaito mana suna fama da matsalar fyade kamar namu ba, idan kuwa za a ce ana yi rubutawa ne ba a yi ba, kenan lokacin da ake suturar da ake zaton ta katange su daga fyaden a zamanin kusa da mu  rubuta mana ne ba a yi ba a,  amma ana yi.

Zamowar shigar banza cikin rukunnan sanadiyyar fyade ya fi tasiri a kudancin Najeriya inda mata ke yin shigar da ba kawai matse jiki take ta nuna surarsa ba, tsiraici ne kai tsaye inda zasu kasa ilahirin jikinsu Kashi uku su bar kashi biyu a bude, wannan lamari tun muna yara al’ummai da masu fada a ji suka koka da shi ba kawai don hasashe daga nesa ba, sai don tabbas alkaluman fyade sun nuna cewa an fi yiwa irin wadannan masu shigar banza fyade fiye da yara kanana da masu sutura. 

Dalilan fyade na da yawa kuma mummunar shiga na cikin rukunin munanan abubuwa da Allah Ya hana, mutunci ya hana, domin har turawa na yaki da sexual harassment wanda mummunar shiga na cikin rukuninsa, amma baya cikin dalilai na gaba-gaba da ke janyo fyade musamman a Arewacin Najeriya domin idan har Alkaluman fyaden a Kano da ke da kason masu lullubi kusan kashi 70% zai haura alkaluman fyaden Lagos wadda ke da masu tsayawa akan titi zigidir haihuwar uwarsu har yau har gobe, to lallai a dena takura kwakwalwa wajen samo dalilan da zasu kai mummunar shiga sahun gaba a cikin dalilan fyade,  shi ma din da yake ba a na kallon matsalar a bangarence ba ne basu kawo shi a layin uziri ba sai a layin kara inganta hanyoyin dakile fyaden da gaske, wato maana, idan mutum yayi fyade ba shi da wani uziri na ganin wata shigar banza, kuma wadannan mutanen na kudu masu alakanta shigar banza da Janyo shaawa, da zasu sami shigar yar Arewa da ake zargi da shigar banza da sam basu ma tuna sutura a dalilan fyade ba. Domin shigar banza a wajensu ita ce wannan siket din matansu ke sanyawa ana hango pant dinsu duk motsawar da suka yi, sannan daga sama ban da Nono babu abinda suka rufe, shi ma rabi da rabi. Shin wannan hukumcin muke son debowa mu ajiye a yankin da mata kashi 90 ke rufe daga samansu har kasansu? 

Wasu dalilai na fyade da bai kamata a manta da su ba sun hada da 

1 Karancin tsaro 

2 Yin laifi a kwana lafiya babu hukumci 

3 Daukar fansa don bata sunan wata yarinya

4 Rashin aikin yi

5 Talauci da ke mika yaran da ake wa fyade zuwa ga hadari

6 Rashin isasshen tsaro 

7 Nisantar halataccen Jima’I 

8 Dalilin DanBarno mai cewa tsadar yardajjen karuwanci na janyo fyade a tsakanin yan cirani 

9 Rashin tausayi da karancin iya rike kai

10 Mai da wanda ake yi wa fyade haja maras rai da rayuwa sai zama abin biyan bukata mai magana

Hanyoyin magance su na bukatar hadin kan mu da nisantar bangaranci. Ba don ba a yi wa wani jinina ba, ko don na kare iyalina daga barazana shikenan na rika jin cewa dukan ya wuce kaina don haka bai shafe ni ba sai a mahangar nazari da hirar da na saba ba. Al’ummarmu ita ce jininmu da iyalinmu, kuma dole mu kare ta mazanmu da matanmu ta hanyoyin yakar fyade kai tsaye.

1 Mu wayar da kan masu boye laifin don su tona.

2 Taya wadanda aka yi wa fyaden fadan kwatar hakki 

3 Taya lauyoyi yakin neman sauya hukumcin fyade a kasar nan daga mai sauki zuwa ga mai tsauri 

4 Yaye duk wata kalmar bata suna daga kan wadda aka yi wa fyade mu dora ta akan wanda yayi fyaden 

5 Tilasta Gwamnati ta dauki mataki ta hanyar yan majalisunmu masu wakiltar mu

6 Samar da tsaro ga wadanda ke fuskantar barazanar fyade 

Ta hanyoyin 

1 Hana talla 

2 Hana aiken yara maza da mata wajajen mutanen da ba a yarda da su ba

3 Samar da ingantacciyar Shiga

4 Tilasta zuwa makaranta

5 Bibiyar halinda yara ke ciki a kowane lokaci.

MATSALOLIN INFECTION GA MA’AURATA MATA DA MATA:-

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.

1)Rashin sanya pant.

2)Barin pant yayi dauda sosai ba a canja ba.

Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.

3)Saka pant a jiqe da ruwa.

4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.

5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa.

6)Rashin aski.

7)Wasa da gaba.

8)Yawan cin `Danyar Albasa.

9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.

10)Dadewa akan Masai ko toilet.

11)Rashin shan iska.

12)Musanyar tufafi.

13)Saduwa da mai cutar.

12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.

ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA:-

1)Yana sa Rashin Sha’awa.

2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.

3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.

4)Yana sa mace ta dinga jinin al’ada baki kirin mai wari.

5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.

6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.

7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.

8)Yana rikitawa mace kwanakin al’adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.

9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.

10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.

11)In yayi karfi yana hana mace haihuwa.

12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

Abin lura:-

Idan mace tayi magungunan Asibiti

da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba,

To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.

- Advertisement -