Shin Real Madrid Za Ta Iya Lashe La liga?  

0
62

Shin Real Madrid Za Ta Iya Lashe La liga?   

A ranar 2 ga watan Mayun shekara ta 2012, Real Madrid ta doke kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao da ci Three-Zero a filin wasa na St Mames ta lashe kofin gasar La Liga kuma na 32 jumulla.

Real Madrid din ta yi nasarar cin kofin kasar Spaniya a lokacin da ya rage saura karawa biyu a karkare wasannin La Liga a lokacin kuma wadanda da suka ci mata kwallayen solar hada da  Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo.

A kakar wasan ce Real Madrid ta hada maki 100 da cin kwallo 121, kuma Cristiano Ronaldo ne ya zama kan gaba a zura kwallaye a raga mai kwallaye 46 bugu da kari a kuma kakar ce Real Madrid ta yi bikin cika shekara 110 da kafuwa a kakar ta 2011 zuwa 2012.

Kungiyar ita ce ta farko da ta hada maki 100 a tarihi da cin kwallo 121 a gasar ta La Liga  haka kuma kungiyar ta yi bajintar lashe wasa 32 da yin nasara a karawa 16 a waje kuma Real Madrid wadda ta lashe La Liga a kakar wasa ta 2011 zuwa 2012 ta bai wa Barcelona tazarar maki tara tsakani wadda ta yi ta biyu.

Jose Mourinho ne ya ja ragamar ‘yan wasa da ta kai Real Madrid ta ci La Liga a kakar, hakan ya sa kocin ya lashe kofin kasar Portugal da Ingila da Italiya da kuma Spaniya sannan Real Madrid mai kofin La Liga 34 jumulla kawo yanzu ta kara lashe biyu a kakar wasa ta shekarar 2016 zuwa 2017 da kuma 2019 zuwa 2020.

What's On Your Mind?