Shin Mendy Zai Iya Maganin Kwallayen Da A Ke Zura Wa Chelsea A Raga?

0
117

A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kwashi kwallaye uku a raga a wasan da kungiyar ta tashi 3-3 da kungiyar kwallon kafa ta Westbrom Albion wasan da a ka yi zaton Chelsea ba za ta iya samun maki ba bayan tun farko an zura ma ta kwallaye uku a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai hakan ya biyo bayan matakin da kociyan kungiyar Frank Lampard ya dauka na ajiye mai tsraon ragar kungiyar na farko, Kepa Arrizabalaga inda ya saka Willy Cabalero a raga kuma aka zura masa wadannan kwallye.

Shin Mendy Zai Iya Maganin Kwallayen Da A Ke Zura Wa Chelsea A Raga?

Dan wasan kasar Senegal kuma mai tsaron ragar kasar Mendy, ya koma Chelsea a satin da ya gabata kuma mai tsaron ragar dan shekara 28 a duniya, ya buga wasanni 25 a tsohuwra kungiyarsa ta Rennes bayan ya je kungiyar daga Reims a shekarar 2019.

An kammala duba lafiyarsa ranar Talata, yayin da kocin Chelsea Frank Lampard ya ce yana so a rika gasa tsakaninsa da Kepa Arrizabalaga, wanda aka saya a kan £71m a shekaru biyu da suka gabata daga Athletico Bilbao.

Kepa ya yi kuskure a kwallo ta biyu da Liberpool ta zura wa Chelase a gasar Firmiya ranar Lahadin satin daya gabata, kuma Lampard ya ce hakan “kuskure ne karara kuma ya kamata a daina kuskure mara kan gado.”

KU KARANTA: Za A Fara Canja ’Yan Wasa Biyar A Kofin Zakarun Turai Da Na Europa

A kakar wasan da ta wuce an ajiye dan wasan na Sifaniya bayan ya rika tafka kura kurai cikinsu har da a wasan karshe na gasar cin Kofin FA, lokacin da aka maye gurbin  mai tsaran ragar kuma  na biyu Willy Caballero, mai shekara 38.

A kakar wasan da ta wuce, Mendy ya hana a zura kwallo a ragar Rennes a wasanni tara a cikin wasanni 24 na Ligue 1 da ya buga, idan aka kwatanta da kwallo takwas da Kepa ya hana a zura a ragar Chelsea a wasanni 33 da ya buga na gasar Firimiya.

Mendy ya tare kwallo kashi 76.3 cikin kashi 100 da aka harba masa kuma ya bari an ci kwallo daya a cikin kowadanne minti 114 sai dai a nasa bangaren, Kepa ya tare kwallo kashi 53.5 cikin 100, sannan ya bari an ci kwallo daya cikin kowanne minti 63.

Mendy, wanda ya buga wasannin kasashen duniya guda takwas, ya zama dan kwallo na takwas da Frank Lampard ya saya tun da aka bude kasuwar saye da musayar ‘yan kwallon kafa a bana kuma a sati mai zuwa zai fara bugawa kungiyar wasa.

What's On Your Mind?