Shin Da Gaske Ne Ummi Zee Zee Na Neman Mijin Aure?

0
152

A shafukan sada zumunta an fara nuna yada cewa tsohuwar Jarumar masana’antar Kannywood ummi zee zee tana neman mijin aure wanda indai zai iya bata abinci da sha komai kankantar sana’arsa zata aure shi kamar yadda zaku gani a wannan hoto.

Shin Da Gaske Ne Ummi Zee Zee Na Neman Mijin Aure?

Sai yanzu nan Majiyarmu ta Hausaloaded ta samu jarumar ta wallafa a shafinta inda ta nuna cewa karya ne ake mata ga abinda take cewa.

“Salam to Nigerians ni UMMI IBRAHIM ZEEZEE ba Dan jarida ko wani da yayi hira dani nace masa ina neman mijin aure karya akemin domin a followers dina daga cikin masu ilimin Wanda suke kula da sa ido a rayuwata gaba daya solar San cewar ina da saurayina da nake sonsa shima kuma yake sona sosai fiye da ko wace mace a duniya bayan mahaifiyarsa Wanda ko gobe nace ya fito muyi aure to zai turo iyayensa gidanmu a mana aure kawai dai good bansa aure a gaba na yanzu ba sai na gama karatuna na DIGREE domin ni a makaranta DIPLOMA kawai nake dashi.Dan haka naji haushi sosai da wannan batun karyar neman mijin da akamin kuma abunda yaban haushi shine :da akace ina neman mijin auren da zai ban ci da sha sai kace wata ALMAJIRA ,to ni ci da sha tuni nafi karfinsu wasu ma ciyar dasu nakeyi nagode #asha ruwa lafiya.”

What's On Your Mind?