Shekara Daya Da Kullen Korona: Yadda Masara Lafiya Suka Sha Bakar Wuya

- Advertisement -

Shekara Daya Da Kullen Korona: Yadda Masara Lafiya Suka Sha Bakar Wuya

Tare Da El-Zaharadeen Umar,

Shekara kwana inji masu iya Magana. Kamar jiya ne gwamnatin Jihar Katsina ta sanya dokar hana fito domin yakin da kuma takaita yaduwar cutar mashoko mai saurin halaka jama’a  ta hanyar kulle mutane tare da takaita zirga zirga ababan hawa sai idan ya zama dole.

Abubuwan ban al’ajabi da ban mamaki kai har da ban tausayi solar faru a lokacin da hukumomi a matakai daban-daban suka kakaba wannan doka ta zaman gida, domin a cewarsu hakan ne kadai zai iya takaita yaduwa wannan cuta mai saurin kashe mutane da ba ta jin magani.

Kamar yadda na ce abubuwa da dama solar wakana, amma dai a wannan bincike na musamman da na gudanar zai fi maida hankali akan jama’ar da suka kasance suna da wata lalura ta rashin lafiya kuma ba su da hali, ma’anin abin hawa da zai iya kai su asibiti domin ganin likita.

Duk da kafa wannan doka ta zaman gida da gwamnati ta yi, bata rufe cibiyoyin kula da lafiya ba, sannan bata hana zuwa asibiti ba ga marar lafiya ba, amma dai duk wanda ya samu kansa a halin rashin lafiya kuma baya da abin hawa a wancan lokacin zai zama abin ban tausayi.

Malam Magaji Magini mazaunin unguwar Malali da ke gefan garin Katsina, ya kasance magidanci wanda yake da mata da take dauke da ciki a daidai wancan lokacin kuma ga rashin lafiya da take fama da ita, sannan baya da abin hawa wanda zai iya kaita asibiti idan bukatar hakan ta ta so, saboda haka ya shiga cikin zullumi kadda haihuwa ta zo wa matarsa cikin dare ga kuma dokar zaman gida.

“Tsakanina da Allah abin da zan iya tunawa recreation da wannan doka ta zaman gida shi ne, akwai wata rana da matata mai dauke da juna biyu sannan kuma bata da lafiya, wata rana da secure, rashin lafiyar ta taso ashe ma haihuwa ce, kuma gashi ana gargadin mu da zaran mun ga alamun haihuwa mu garzaya asibiti musamman ita da ma tana fama da rashin lafiya” inji shi

Ya cigaba da bayani kamar haka, “lokacin da wannan ciwo ya so, babu yadda zan yi domin daman idan irin haka ta faru ina zuwa bakin baban titi in samu a daidaita, ta zo har gida mu dauke ta zuwa asibiti, sai na yi tunanin yanzu ya ya  zan yi ke nan? Domin ganin irin halin da wannan baiwar Allah ta shiga zai kawai na impolite na rasa me ke mani dadi”

Babu shakka daga yadda yake magana, lallai yana san matarsa wanda a wannan lokacin ne zata yi masa haihuwar farko, kuma ya ce duk wani abu na tarbar haihuwa abakin gwargwado ya tanada, duk da kasancewarsa ba mai hali ba.

To sai dai fa yana cikin hali ni ‘ya su da kuma zullumi recreation da makomar matarsa akan zuwa asibti kuma ciwo ya sanyo ta gaba yana neman kasheta, ya fada da bakinsa ya ce “idan har wannan baiwar Allah ta rasa ranta da abinda ke cikinta lallai akan hukumomi zan dora wannan alhakin ba akan korana ba.

Da yake takaita wannan labari na shi da yake yi wa lakabi da korona ta so kashe mani mata, amma dai sai ta dauki jaririn, ya yin da yake karin haske akan yadda ya samu taimakon wani bayan Allah da bai dade da dawowa cikin wannan unguwa ba, wanda da taimakonsa ne aka kai matar asibiti bayan ta galabaita har ta fara fita daga hayyacinta in ji Magaji Magini

Yace koda suka je asibitin solar sha tirka-tirka da jami’an lafiyar domin a cewarsu ba anan matar take yin awo ba, shi kuma ya kowata ne wajan domin ceton ranta da kuma abinda take dauke da shi, saboda haka duba da irin yanayin da ake ciki yasa bai tsaya tunanin ina ne ya kamata ya kaita ba.

Wannan labari dai baki dayansa ya tsayawa wannan bawan Allah acikin zuciya duk lokacin da aka ambaci sunan korona, ya ce babu abinda yake tunani sai jaririn da ya rasa a sanadiyar dokar zaman gida da gwamnati tasa domin dakile wannan cuta ta korana barus a jihar Katsina.

Ba labarin Malam Magani kadai nake da shi ba, wani bincike ne da na gudanar sanadiyar wani taron karawa juna sani da na halarta a garin Kano wanda wata kungiyar mai suna “Paged Iniatibe” suka shiryawa manema labarai dangane da wannan batu na cutar mashoko, saboda haka zan cigaba da kawo hirararki da kuma bayanan da na tattara a lokacin wannan bincike nawa, na tabbtar mai karatu sai koyi darasi daga abinda zai karanta dangane da wannan al’amari na dokar zaman gida

Shi kuma Malam Akilu Alarama, yaransa mai suna Ibrahim dan shekara biyar ya fada rijiya a daidai wannan lokaci, bayan an fito da yaron sai ya kasance mai mutu ba amma dai ya sha wuya iya wuya saboda haka babu abinda ya rage illa a nufi asibiti da wannan yaro.

Da yake bada labarin yana kuka ya ce lokacin da na samu mai adaidaita sai kawai na tsayar da shi na gaya masa abinda ya faru da da na, amma ya taimakai ya kaimu asibiti, ashe shi wannan mai adaidaita ya fito ne ba bisa ka’ada ba saboda haka ya ci karo da jami’an tsaro masu yin sintirin don ganin abin doka da oda ta zaman gida, inda da kyar ya kwaci kansa.

Ganin halin da wannan yaro ke ciki yasa mai tuka wannan adaidaita mai tsaya yi mani wani bayani ba, sai kawai ya tuka wannan adaidaita domin zuwa asibiti a duba wannan yaro, bisa rashin sa’a ashe jami’an tsaron da suka yi artabu da wannan mai adaidaita solar ja masa kunne cewa lallai ya koma gida kadda su sake haduwa da shi zai kuka da kanshi, cikin rashin sa’a suka sake haduwa da mai adaidaita ya dauko marar lafiya.

Alarama Akilu ya cigaba da bada labari yana cewa ban san abinda ke faruwa ba, sai kawai na ga wannan yaron da ke tuka a daidaita ya dauke hanyar ya shiga wani lungu da mu, maimakon hanyar zuwa asibiti, cikin sauri na ce masa haba Malam babar asibiti zaka kaimu fa, ashe wadannan jami’an tsaro suke biyo shi ba tare da sanin su wa ya dauko ba.

Anan zan tsaya Insha’Allahu sati mai zuwa zan cigaba da wannan bincike nawa, inda za aji labarai masu so sa zuciya kwarai da gaske, sannan zaku ji ba’asin hukumomi recreation da wannan al’amari, hatta Masana solar fide biri har wutsiya akan yadda za a tunkari irin wannan matsala anan gaba idan ta sake tasowa, sannan zaku ji yadda su kan su jami’an lafiya suka shiga wani hali a dalilin wannan cuta ta korona

 

- Advertisement -