Sheikh Ja’afar Na Daga Cikin Hazikan Mutane 60 Da Allah Ya Albarkaci Nijeriya Da Su

0
24

Daga Abdulrahman Muhammad Sharada
Alwazwazee

Jiya da misalin karfe biyar zuwa shida na yamma na shiga unguwarmu ta Sharada sai na ci karo da Kabiru Hussaini Madaki, wani cikakken dan boko ne kuma hazikin matashi mai muradin zama Farfesa, sai na ga wani katon littafi a gurinsa mai suna (the nation builders @60) mutum 60 da suka gina Nijeriya a duniyar ‘yan boko da hazikan mutane.

Sanarwa Daga Darakta Aminu Saira Akan Film Din Labarina

Littafin ya tattatara hazikan mutane guda sittin wadanda babu kamarsu a Nijeriya a bangarori da dama, kuma wadanda suka hidimtawa kasarsu da kwakalwarsu da aljihunsu da iliminsu.

Abinda ya ba ni sha’awa ganin sunan Malam Ja’afar da na yi duk da wadanda suka rubuta liffafin su biyar mutum daya ne musulmi, solar zabe shi a matsayin Malami mai kishin Nijeriya da kuma son kawo sauyi.

Na yi matukar bincike akan wannan zabin da suka yi masa sai na ga tabbas solar yi zabi mafi girman daraja da cancanta, musamman da na tuna rayuwarsa yadda ya gudanar da ita.

Ya Allah ka jikan Malam Ja’afar ka sa aikinsa na alkari ya bi shi. Amma wallahi mun yi babban rashi wanda har yanzu muna jin wannan radadi, Allah ka wulakanta wadanda suka yi sanadiyyar daukar ransa, Allah ka lalata al’amuransu.

Ya hidimtawa addinin Allah kuma aka kashe shi akan zalinci, har yanzu idan ina jin Malam sai na ji kamar har yanzu da rayuwarsa, tabbas mun yi rashi kuma wallahi bazamu yafe ba, har yanzu ina tuna gani na da shi na karshe a masallacin Usman bin Affan na Gadon Kaya a Kano.

What's On Your Mind?