Sheikh Dahiru Bauchi Ya Jadadda Batun Sallar Idi A Yau Laraba

- Advertisement -

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Jadadda Batun Sallar Idi A Yau Laraba

Daga Khalid Idris Doya,

A bisa bayanan da wasu suka kama yadawa na cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a cigaba da Azumi, batun ba gaskiya ba ne.

Almajirin Shehin sun tabbatar da cewa wasu ne da batun Sallar Idi a Yau Laraba bai musu dadi ba suka kama yadawa domin karkatar da hankalin jama’a.

“Mu yanzu muna kan shirin Sallar Idi ne kamar yadda aka sanar tun jiya. Muna sake nanata batun Sallar Idi da karfe 9:30 a Gidan Sheikh Dahiru Bauchi da ke kan titin Gombe a cikin garin Bauchi,” Inji Hadimin Shehin.

Solar tabbatar da cewa Sallar Idi na nan karfe 9:30 na safiya yau din nan.

- Advertisement -