Shawarwarin Likitoci Ga Masu Azumi

0
79

Shawarwarin Likitoci Ga Masu Azumi

Daga Maigari Abdulrahman,

Azumi kamewa ne daga ci da sha na tsawon kwana 29 ko 20. Abinda ke biye shawarwari likitoci ne ga masu azumi da kuma mata masu ciki, hadi da abubuwan da ya kamata mai azumi ya yi musamman a lokacin buda baki.

Dakta Sulaiman Auwal, masanin harkar kiwon lafiya kuma likita a asibitin ‘Bauchi Specialist Hospital’ ya yi bayani kan lafiy da azumi, inda ya ce azumi na kara lafiya, kuma yana katange mutum daga kamuwa da wasu cututtuka, kamar ciwon suga.

Haka kuma, yana rage kiba a lokaci guda kuma yana kara kaifin basira da karfin kwakwalwa tare inganta kuzarin jikin mai yin azumi.

To sai dai, likitan ya shawarci iyaye masu shayarwa da su dakatar da yin azumi yayin shayarwa, domin hakan kan iya raunata jikinsu, a yayin shayarwar, jikinsu kan bukaci abinci fiye da a baya, ga jariri ga kuma su kansu, in ji shi.

Wahalar daukar ciki da rainonsa har zuwa haihuwa, ya kan sanya gajiya a jikin macce tare da raunatawa, saboda haka ne mace ke bukatar abinci na musamman mai gina jiki a yayin da take da juna-biyu da kuma bayan haihuwa, in ji likitan.

Haka ma, a likitance, tsoffi masu shekaru suna daga cikin gurbin wadanda a ke shawartar su aje azumi duba ga yanayin jikinsu, sakamakon raunin garkuwar jiki da ke tattare da tsufa.

Har wa yau, likitan ya shawarci mutane da su guji cika-ciki yayin buda baki, ya kuma bada shawara kan abinda ya fi dacewa yayin shan ruwa zuwa lokacin kwanciya.

“A guji cika-ciki yayin shan ruwa, a maimakon haka a bada tazarar cin abinci. Cika-ciki gam yayin shan ruwa kan wahalar da jiki narkar da abinci. A maimakon haka, ana iya farawa da ‘yayan itace, wani abu mai ruwa ko abinci marar nauyi mai karancin “Carbohydrate da protein”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “ Abu ne mai wahala ilmantar da al’umma kan harkar kiwon lafiya, amman kiyaye ka’idojin likita da shawarwarisu na taimakawa matuka wurin inganta lafiyar mutum. Yana da muhimmanci mutum ya kula da yanayin abincin da zai saka wa cikinsa.”

Shima a nasa bangaren,liktan abinci, Ibrahim Muhammad Lade, ya ce mai yin azumi na bukatar cike gurbin abincin da yake rasawa a yayin azumi.

Likitan, ya bada shawarar gabatar da ruwan dimi yayin buda baki domin gyaran ciki gabanin abinci. A lokaci guda kuma, ya ja hankali kan anfani da ruwan sanyi masu sanyi sosai. Idan ya ce, idan ma har dole sai mutum ya fara da ruwan sanyi, to kada ya cika ciki makil lokaci daya, hakan kan iya raunata jiki ya kuma jefa wa mutum kasala.

“Fara buda baki da ‘yayan itace abu ne mai kyau, daga baya kuma sauran abubuwa kamar koko da sauran su sai su biyo baya. Cin abinci mai nauyi kan wahalar da na’urar jiki narkar da shi, wanda hakan ke daukar akalla awa biyu.”

“A guji cika-ciki tam, yin hakan kan sanya kasala da bacci, sai ya zama mutum ya kasa yin ibada cikin dare saboda nauyin jiki sai dai bacci, kuma yana da illa kwanciya bayan cin abinci,” in ji likitan.

A ci gaban bayanin sa, ya jaddada anfanin azumi ga jiki, inda ya ce jikin mutum kamar injin ne, yayinda ya ci abinci, jikin ya kan sarrafa shi daidai da bukata, yayin da wani kaso ke zuwa a ma’ajiyar jiki. Amman a yayin azumi, jikin mutum yakan samu damar sarrafa abinci ba tare da cikar ciki ba, wanda hakan yaakn ba jikin damar sarrafawa abinci daidai misali ba tare da gajiyawa ba sabanin wani lokacin.

Ya jaddada bukatar ajiye azumi ga mata masu ciki, wanda ya ce mai ciki na bukatar cin abinci fiye da baya, domin abinda ke cikin cikinta, yin azumi kan iya cutar da ita ko abinda ke ciki, kan haka ajiye azumin shi ne ya fi dacewa a likitance..

A yayin da mace ke da juna biyu, gangar jikinta kan bukaci abinci fiye da lokacin baya, tana bukatar ninka ”calorie” zuwa akalla kaso 200 zuwa 500, wanda hakan ba zai taba samuwa ba ga mai azumi, kuma zai zama illa gareta da abinda ke ciki, kan haka dole ta ajiye azumin domin cceton rayuwarsu, in ji likitan

A nata jawabin ita ma, Dakta Alaba Fumiola, ta ce dayawan mutane kan kuskure a lokacin Ramdan, ta hanyar cika-ciki yayin buda baki.

“Gaskiyar magana shi ne, cika-ciki da abinci gam na da illa. Shinkafa, tuwo, koko duk a lokaci daya? Lalle hakan ba taimakawa jiki ba ne kuma yana da illa. Ta hakan ne wasu ke yin kiba yayin azumi, “ in ji likitan

“Mai azumi na bukatar cin abinci daidai misali ba tam ba. Haka ma yana bukatar hada nau’ukan abinci mabanbanta ba daya ba, kamar ganye, ‘yayan itace, hatsi, nama da sauran su.”

“A misali, idan za ka ci shinkafa, akwai bukatar saka nama ko kifi a ciki, tare da kuma ganyatyaki da kuma mai, ga kuma ruwa da za a yi anfani da shi, hakan zai hada zai bayar da abinda ake bukata ga jiki.”

Ta ce, “ Za ka ga wasu solar hada abinci ko abin sha iri daya a lokaci guda, misali kunu, zobo da shinkafa. Wannan duk nau’in abinci daya ne kuma ba abinda ake bukata ba kenan.

Baya ga abinci, Likitar ta shawarci masu azumi da motsa jiki, wanda ta ce, duk da azumin, jiki na bukatar motsa shi.

“Bai kamata mai azumi ya daina motsa jiki ba ya koma zaman jagwam a wuri daya ba a ofis, wurin aiki ko gida ba. Akwai bukatar ko da dan mika jiki ne ba yin zaune guri daya ba. Sai dai kuma ba a bukatar motsa jiki mai nauyi.”

Ita ma a nata jawabin, ta shawarci mata masu juna biyu kan ajiye azumi, ind ta ce rashin ajiyewar yana da illa kuma zai iya shafar uwar da kuma abinda ke ciki

“Wasu matan ba sa bin shawarwarin likitoci na ajiye azumi yayin da su ke da juna biyu. Rashin cin abincin ki na da illa ga jinjinrin, domin idan har ba ki ci abinci ba, to shima ba zai samu abinci ba.”

 

What's On Your Mind?