Shawarwari Ga Ma’aurata Kafin A Daura Muku Aure

- Advertisement -

Shawarwari Ga Ma’aurata Kafin A Daura Muku Aure

Daga Yusuf Shuaibu

Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa daura aure yana nufin kulla wata alaka ce da Allah ya yi umarni da ita.

Gaskiya ne cewa aure ya kasance daga cikin dabi’u na dan’adam, to amma duk da hakan Allah ya tsarkake wannan alaka wacce daga karshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a dauki wannan alaka a matsayin wani abu mara muhimmanci ba.

Dole ne ku yi iyakacin kokarinku wajen kare wannan sabuwar alaka, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku yi amfana da ‘ya’yanta.
Babu shakka miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nitsuwa gare su bayan solar gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata bukatuwa ce da ma’auratan suke bukatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna bukatar farin ciki da yanayin da yake samar da hakan. Mai yiyuwa ne macen ko namijin su kasance ‘yan kasuwa, ko kuma ‘yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu su kan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna bukatar yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata bukata ce ta wuce guri ba, a’a, a dabi’ance haka lamarin yake.

Hakika lamarin ba shi da alaka da abin hannun da mutum yake da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su dandani dadin zamantakewar aure ba; rayuwarsu ta kasance cikin kunci, cike take da hassada da haramtattun bukatu da fata. Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, mai yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi mara hakuri ko kuma malalaci. Don haka dukiya, mukami, zaman birni ko kauye ba za su canza yanayin zamantakewar iyalai ba matukar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma’auratan biyu.

Abu na biyu da zan gaya muku shi ne, yana da kyau ku fahimci cewa wadannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi kokari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma’auratan su so junansu. Kamar yadda ake cewa ne: “Ba a iya tabbatar da so da kauna ta hanyar karfi da tursasawa”, lalle haka ne don kuwa so kamar karamar bishiya ce, dole ne a ba ta ruwa da kula da ita, don haka duk wani abin da za ku yi wajen kula da girman wannan bishiya dole ne ku yi hakan wa kaunarku. Hakan kuwa yana hannayenku ne ya ku matasa. Hanyar da za ku bi wajen cimma wannan abu ita ce ta hanyar kauna da biyayya ga junanku da kuma nuna wa abokan zamanku hakikanin so da kulawa.

Babu makawa, kusan dukkan kiraye-kiraye da umarnin da Musulunci yake bayarwa dangane da sanya Hijabi yana yinsu ne, saboda kare wannan alaka ta aure. Don haka idan har, a matsayinku na matasan da za su yi aure, ba ku kula da hijab a lokacin da kuka fita waje, ko kuma kuka bari idanuwanku suka koma kan wasu matan ko kuma mazan, zukatanku suka koma ga wasu sabanin abokan zamanku na aure, idan kuka bari har kuka kulla alaka da wasu mata ko mazajen da ba naku ba wadanda kuke gamuwa da su a wajaje daban-daban, to babu makawa aurenku na iya shiga cikin mawuyacin hali. Da farko dai abokin zaman naku zai/za ta fara rasa irin sha’awar da ke jawo hankalinsa/ta zuwa gare ka/ta da ke haifar da so da tausasawa.

Wani abu kuma da yake da muhimmanci ku fahimta shi ne cewa babu wani mutum, namiji ne ko mace da ba shi da irin wadannan rauni da kura-kurai, babu wanda yake ya cika komai. Hakan ne ma ya sa za mu ga cewa dokokin Musulunci suna kokarin kiyaye alaka ne ta aure.

Hijabi ma don haka aka yi umarni da shi, don ka da mace ta bude jikinta ga wasu na daban, ka da ta shigo cikin mutane ba tare da suturan da ta dace da mutumci da girma ba, don ka da ta ta da hankulan wasu na daban, dukkan wadannan abubuwan janyo hankula an kiyaye su ga abokin zamanta mijinta.

Don haka ya zama dole, tun ranar farko na auren, ma’abutan biyu su yi kokari wajen kare wannan so da kauna da Allah ya dasa cikin zukatansu. Ya kamata su yi kokari wajen kara wannan kauna da soyayya da kuma karfafa su. Hanyar cimma hakan kuwa, kamar yadda na fadi ne a baya, ita ce ta hanyar taimakon juna da kiyaye mutumci da manufofin juna. A matsayinsu na ma’aurata biyu, dole ne su kiyaye sirrin juna, ka da su fade su ga wasu ko da kuwa dangi ko na kurkusa da su ne, dole ne ku kiyaye irin shigar da kuke yi. Idan har kuka kiyaye hakan, to babu makawa za ku ji dadin zaman aurenku.

Abu na uku da nake son nuni da shi, shi ne muhimmancin sassauci da yafewa juna, duk da cewa sassauci ba abu ne da ke da kyau a dukkan lokuta ba na rayuwa ba, to amma mafi kyaun sassauci da yafiya a kan yi shi ne a rayuwa ta aure. Don kuwa, a matsayinku na sabbin amare da angwaye, za su ci gaba da fahimtar junanku da kuma dabi’un juna kusan kullum. To lalle ka da irin wadannan sabbin abubuwa su kashe muku gwiwa, don kuwa babu wani mutum a duniyan nan da ya cika goma. Don haka dole ne ku yi hakuri a lokacin da kuka ga wani abin da ya bata muku rai, ko kuma wasu maganganu marasa dadi, don kuwa hakuri da kau da kai su ne kawai maganin wadannan abubuwa.

Abu na gaba kuma shi ne batun jin dadi, bukukuwa da sauran kashe kudade na gaira ba dalili a lokacin aure. A lokuta da dama na sha magana kan kokarin takaita kudin sadaki, to sai dai hakan ba wai yana nufi cewa idan aka ba da sadaki mai yawa aure ya baci ba ne. A’a, abin da dai na ke kokarin nunawa shi ne, cewa aure dai wata alaka ce ta dan’adam, wato wani alkawari ne tsakanin rai da zuciya, don haka idan har batun makudan kudade suka shigo cikin, to zai tashi daga wannan ma’ana tasa ya koma zuwa ga ma’ana ta kasuwanci, wato saye da sayarwa a kasuwa. Baya ga haka kuma irin wannan yawan sadaki zai kara dora nauyi kan mazaje masu son yin aure. Misali wata mace tana iya cewa ai sadakin da aka ba wa wance kaza ne kudi da yawa, don haka ni ma dole ne sadaki na ya kasance kaza wato ya fi na wancen. Don haka ne na ke shawartarku da ka da ku sanya idanuwanku kan yawan sadaki. Ku yi kokari ku takaita shi dai-dai gwargwado ka da ku wuce hakan.
Abu na karshe da ya kamata ku sanya cikin zukatanku shi ne, batun karfafa juna kan kyawawan dabi’u da kula da hukumce-hukumcen Musulunci.

Ku yi kokarin ku ga kun kara karfafa imaninku ta hanyar aurenku da kuma wuraren da kuke, shin ofishi ne ko kuma wajen da kuke aiki, ko wajen wasanni da dai sauransu. Don kuwa ta hanyar dabi’unku za ku iya janyo hankulan wasu zuwa ga addini, ta hakan za ku iya sake rayar da koyarwar Musulunci a zukatan sauran mutane da kuma karfafa su. Babu makawa wadannan abubuwa za su kasance masu amfani ne gare ku da kuma al’ummar da kuke ciki.
Ina fatan wadannan shawarwari nawa za su kasance muku tamkar samun kyakkyawar rayuwa ta aure.

 

- Advertisement -