Sharhi:Rayukan Palasdinawa Musulmi Ma Na Da Daraja

- Advertisement -

Sharhi:Rayukan Palasdinawa Musulmi Ma Na Da Daraja

DagaL ubabatu Lei

Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, rikicin da ya barke tsakanin Palasdinu da Isra’ika ya yi ta tsananta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari, tare da ji wa daruruwan mutane raunuka, musamman ma Palasdinawa da suka hada da mata da yara. Halin da ake ciki a yankin ya yi matukar jawo hankalin kasa da kasa.

A matsayin kasar Sin na jagorar karba karba ta kwamitin tsaron MDD a watan Mayun nan, Sin din ta yi duk mai yiwuwa wajen kiran tarukan tattaunawa na gaggawa guda 2, domin shawo kan kara tabarbarewar yanayin da ake ciki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, sai dai kuma tarnakin da aka fuskanta daga bangaren Amurka, ya sanya har yanzu kwamitin na tsaro bai cimma daidaito a kan batun ba. A daya bangaren kuma, Amurka tare da Jamus, da Birtaniya da wasu sauran tsirarun kasashe, na fakewa da batun hakkin bil Adam, wajen amfani da sunan MDD, suna kiran wani taro maras ma’ana, wai da sunan tattauna batun Xinjiang.

To, tambaya a nan ita ce, a yanzu da ake dauki ba dadi tsakanin Isra’ila da Falasdinu, kuma al’ummar Falasdinawa musulmi masu yawan gaske, ke fama da tasirin hare hare, Amurka wadda a cewarta ta fi kowa damuwa da hakkin musulmi, ta kawar da kan ta, duk kuwa da cewa batu ake yi na rayuwa da mutuwa, shin akwai bambancin musulmi Palasdinawa da musulmin jihar Xinjiang? Ko kuma hakkin musulmi Palasdinawa ba shi da muhimmanci?
Lalle, ba hakkin musulmi kasar Amurka take damuwa ba. A hakika, Amurka da take cewa ta fi kowa damuwa da hakkin musulmi daidai ta kasance kasar da ta fi yawan kisan musulmi a duniya. Sanin kowa ne yadda Amurka din ta tayar da yaki a kasashen Iraki da Libya da Syria da Afghanistan da sauransu da sunan “yaki da ta’addanci”, ya yi sanadiyyar mutuwar al’ummar musulmi sama da miliyan, a yayin da wasu miliyan gomai suka rasa muhallinsu.

Misali a kasar Afghanistan, yau da shekaru 20 da suka wuce, Amurka ta kaddamar da yaki a kasar, kuma bisa ga wani shirin kididdigar asarorin yaki da jami’ar Boston ta gudanar, tun daga shekarar 2001 kawo yanzu, yakin da Amurka ta yi a Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dubu 241, ciki har da fararen hula sama da dubu 71.

Ko a birnin Kabul, babban birnin kasar ta Afghanistan, jama’a tuni suka saba da fashewar boma-bomai da ma hare-hare da ke faruwa a kullum. Ga shi yanzu, Amurka na neman janye jikinta daga wannan mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki, amma ga abin da ta bar ga al’ummar kasar Afghanistan. A ranar 1 ga wata, Amurka da na NATO suka fara janye sojojinsu daga Afghanistan din, kuma yanayin tsaro a kasar ma ya fara tabarbare nan da nan.

A ranar eight ga wata, an samu hare-hare a kusa da wata makarantar da ke Kabul, wadanda suka halaka mutane sama da 80, tare da jikkata wasu sama da 100. Ban da Afghanistan, ga kuma halin da Iraki da Syria da Libya suka shiga, wadanda Amurka ta taba “damuwa da hakkin musulminsu”.

Bari kuma mu duba jihar Xinjiang ta kasar Sin da Amurka ke “damuwa”, inda tun daga shekarar 1990 zuwa ta 2016, an samu dubban hare-haren ta’addanci, wadanda suka halata daruruwan mutane tare da jikkata wasu dubbai. Sai dai a lokacin, Amurka da sauran kasashen yammaci solar nuna halin ko-in-kula. Ga shi kuma bisa kokarin da kasar Sin ta yi, cikin shekaru sama da hudu da suka wuce, ba a kara samun harin ta’addanci ko guda a jihar, inda al’umma suke rayuwa cikin kwanciyar hankali da walwala, amma kuma hakan ya jawo damuwar Amurka da sauransu. Shin me suke damuwa a kai? Lalle, ba hakkin dan Adam ba ne. A hakika, suna fakewa da sunan “hakkin bil Adam”, a yunkurin tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin da ma dakile ci gaban kasar.

Amma dai, karya karya ce, kuma gaskiya ba ta boyewa. Al’umma masu fama da talauci sama da miliyan uku a jihar Xinjiang dukkansu solar fita daga kangin da suka samu kansu a ciki, kuma akwai masallatai sama da dubu 24 a jihar, wato ke nan ko wadanne musulmi 530 suna da masallaci guda. A jihar kuma, ana amfani da harsuna 7 wajen koyarwa a makarantun midil da na firamare, a yayin da kuma ake watsa shirye-shiryen talabijin da na rediyo da harsuna biyar na kananan kabilu. Baya ga haka, a cikin shekaru sama da 40 da suka wuce, yawan al’ummar Uygur na jihar Xinjiang ya karu daga miliyan 5.55 zuwa miliyan 12.eight, adadin da ya ninka har sau daya.
Abin farin ciki shi ne, karin al’umma suka samu fahimtar gaskiyar yanayin da ake ciki a jihar Xinjiang, tare da gane fuskoki biyu na Amurka a kan batun hakkin bil Adam.

Tashar intanet ta “Africa-China Evaluation”, ta wallafa wani bayani mai taken “Me ya sa kasashen Afirka suka goyi bayan China, amma suka ki yarda da kasashen yamma kan batun hakkin dan Adam”, inda a ciki aka nuna cewa, zargin da kasashen yamman suka yiwa kasar Sin, na cewa wai tana “kisan kare-dangi”, da tilastawa ma’aikata aiki a Xinjiang, babbar karya ce zalla, kuma ainihin makasudin su shi ne tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da hana ci gaban kasar. Bayanin ya kuma ce, kasashen da suka zargi kasar Sin, su ne suka aikata munanan laifuffuka a fannin keta hakkin ‘yan asalin Afirka, don haka ba su cancanci su soki lamarin sauran kasashe ba. Kaza lika kasashen Afirka suna goyon-bayan kasar Sin kan batun hakkin dan Adam, saboda Afirka da Sin duk solar taba jin radadi a jikinsu, na irin yanayin da kasashen yamma suka haifar musu.

Yanzu haka rikici na ci gaba da tabarbarewa a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wanda ke haddasa karin hasarorin rayuka, kuma akwai alamar habakar yaki zuwa sauran sassa. A shawarwarin gaggawa da kwamitin tsaron MDD ya kira a baya, a matsayinta na kawar Isra’ila, a yayin da Amurka din take hana cimma daidaito kan daukar matakai kan rikici, kasar da ke “damuwa da hakkin musulmi” ko ta gane cewa, rayukan Palasdinawa musulmi ma na da kima?(Lubabatu Lei)

- Advertisement -