Sharhin Rubutacciyar Wakar ‘Azumin Yara’ Ta Nasir G. Ahmad  

0
84

Sharhin Rubutacciyar Wakar ‘Azumin Yara’ Ta Nasir G. Ahmad   

Wakar azumin yara waka ce da take da bangarori biyu, bangare na farko yana bayani kan wadanda azumin watan Ramadhan ya wajaba a kansu, da wadanda shari’a ta yi sauki a kansu da ma wadanda ya sauka a kansu gaba daya. Bangare na Biyu wanda shi ne babban jigon Wakar, shi kuma yana bayani ne a kan matsayin azumin yara a shari’a, da kuma gwadaben da ya kamata a dora yara a kai don su dabi’antu da yin azumin har su saba da shi tun kafin alkalami ya hau kansu.

Fasihin sha’iri kuma masani a fagen rubutacciyar waka, kuma marubucin littafin koyon rubutun waka mai suna ‘Guzurin Marubucin Waka’ wato Malam Nasir G. Ahmad ne ya rubuta wakar ta ‘Azumin Yara’. Bayan haka Malam Nasir marubucin hikaya ne, da ya kware a fassara har ya fassara littattafan larabci zuwa harshen Hausa, wadanda suka hada da: Sha-Alwashi, da Abu Firas, da Dare Dubu Da Daya, da dai sauransu.

Wakar azumin yara da Malam Nasir G Ahmad ya rubuta kuma ya wallafa ta a shafinsa na fb a ranar Litinin 19/04/2021. Waka ce mai baituka 27, kuma kowanne baiti daya yake sa dango biyu. Ga dai cikakkiyar wakar kamar haka:

 

 

AZUMIN YARA

 

1) Allahu sarki mai niya,

Hikima ka ba ni a rayuwa.

2) Azumi ga yara zan batu,

Domin gudun rafkannuwa.

 

three) Azumi farilla wajibi,

Ga dukan musulmi ‘yan uwa.

four) Maza da mata ba rabe,

Amma ga mai hankaltuwa.

5) Majnunu ba azumi ga shi,

Zai ci ya sha ba damuwa.

6) Haka nan ga yara ƙanƙana,

Tsoho tukuf har tsohuwa.

7) Yaro gaban yai balaga,

Azuminsa bai shar’antuwa.

eight) Don babu alƙalami bisa,

Kayinsa don sauƙaƙuwa.

9) Sai dai akan horar da shi,

In an ga ba zai ƙwaruwa.

10) A rabin wuni in ya matsu,

Ɗa’am a ba shi ya sha ruwa.

11) Da hakan ga zai saba da yi,

Wata ran ya zam kammaluwa.

12) Ladan iyaye nasa ne,

Ga uwa uba kan basuwa.

13 Bisa ga sanya shi bisa,

Hanyar ƙwarai mai haskuwa.

14) A bar matsa mar kan ya yi,

A bi shi sannu da nutsuwa.

 

15) Balle idan har za a sa,

Shi ayyuka na hidimtuwa.

16) A zam yabon sa idan ya kai,

A ba shi kayan shan ruwa.

17) In an ga zai rame ƙwarai,

A tsayar da shi yai hutuwa.

18) Ƙarfi idan har ya mayar,

La ba’asa yai komuwa.

19) Manufa ya zam saba da yi,

Kafin ya kai ga balagtuwa.

20) Duk san da ya ce za ya yi,

A bar shi kar ai hanuwa.

21) In ya gaza kaiwa kuwa,

Gare shi ban da tsanantuwa.

22) Aikin ibada kwai wuya,

Yaro a sannu ka sabuwa.

23) Allah ya ba mu juriya,

Yara mu tarbiyyantuwa.

24) Su zamo mutane na ƙwarai,

A nan gaba su nagartuwa.

25) Allah ka karɓi dukan iba-

darmu gare ka ta amsuwa.

26) Azumi ya cece mu idan,

Mun zo a ranar tsayuwa.

27) Mai baitukan nan Nasiru,

Ahmad ne dan uwa.

 

What's On Your Mind?