Sharhin Labarin “Daga Kawai Na Ce A’a”

- Advertisement -

Sharhin Labarin “Daga Kawai Na Ce A’a”

Daga Auwalu Garba Danbarno

 

SHIMFIDA

Marubuci Shi ne Ubangijin Rubutunsa, shi ne mai kashewa da Rayawa. Zai iya mayar da mutum na kirki ko na banza duk a cikin labarinsa. Hakan na faruwa ne ta hanyar Salo da kwarewa. A cikin hikima da dabaru ba tare da makaranci ya fahimta ba, zai ji ba ya kaunar wane ko ya fi kaunar wance a cikin labarin da yake karantawa. Duk labarin da ya rubutu, makaranci ba zai taba kauka cewa wannan labarin kaga shi aka yi ba. Mu dauki misalin Littafin :Yar Tsana na Malam Ibrahim Sheme. Makarantan da suka yi kuka ba za su lissafu ba.

Ina yawo a kafar fb na ci karo da wani rubutu da na ga ya kamata na yi gyara mai taken DAGA KAWAI NA CE A’A. Kodayake mun shigo zamanin da kowa sunan sa marubuci, duk da haka dole mu yi gyara da jan-hankali da kuma nusarwa a duk abinda ya gifta ta gabanmu.

Labarin Wasu Jaruman Marubuta ne biyu. Gago da Kuma Rakiya Ado Magashi. Labarin ne mai salon da jarumi ke bayar da labarin da kansa. Rakiya Magashi ita ke bayar da Labarin mu’amalarsu da Gago. Ba a bayyana sunan Gago na Gaskiya ba a labarin.

Jarumar ta yi kokarin tsarkake kanta da kuma nuna Gago a mutum mara mutunci mara tarbiyya kuma Gogagge a Iskanci. Rashin Dabara da rashin iya hannu, ya sa garin kokarin nuna rashin tarbiyyar Gago, Jarumar ta yiwa kanta wasu raunuka da ba za su warke a idon manazarta ba.

 

Farkon Labarin

“Ranar da na fara ganin Goga na yi masa kallon kima da mutunci. Mun hadu ne a gurin taron da kungiyarmu ta marubuta ta shirya.”
“Gani na biyu da na yiwa Goga Shi ne gurin haduwar mu a wani taron da jarumi ya shirya a garin su na Cigari”
“Bayan tashi daga taron Goga ya yi min wata magana da ta sa na tsaya kallon shi, cewa ya yi ke Magashi me ya sa ba ki ci cincin ba a lokacin da kowa ke ci koda yake na lura kin fiye yanga. Na ji nauyin wannan kalmar da ya furta kaina domin sai na ga kalma ce da ya dace Saurayi ya fadawa Budurwa ba ni matar aure ba.

Abinda ya fi damu na shi ne yadda na ga ya na yiwa wasu Shagube tare da ci masu zarafi.”

Ina ciga ba da kallon abinda Goga ke yiwa mata da daidaikun mazaje, abinda na lura idan zai yiwa maza sai dai wanda ya raina, mata kuma ya fi wa wadda ba ta da miji Bazawara ko Budurwa.

Idan har Jarumar mai mutunci CE a matsayinta na Matar aure tun daga nan ya kamata ta nesanta kanta da Goga tunda ta lura bai da Mutunci. Amma ina wai sai ta ci gaba kuma da hulda da shi.
ME YA HANA MAGASHI YANKE HULDA DA GOGA?
Ni ina ganin fa a yadda Jarumar ta ke bayar da labarin, akwai alamun zubi da kirar Goga solar kwanta mata a rai. ji abinda ta fadi a wani saashi na labarin.
” A taron su Goga ne manyan hadimai, don haka motarmu na tsayawa da shi mu ka fara Karo. Ya dauki wankan kwat da wando Bakake.”
Dubi wannan maganar. ya dauki wanka. Babu macen da za ta furta cewa an dauki wanka sai idan wankan ya burge ta. Matar Aure ce fa ke fadin mijin wata ya dauki wanka. sai ta ci gaba
” Tumbinsa ya sha Balat ga wani lakatayen ya daura tamkar manajan banki. Ya tare mu da fara’a aka gaggaisa, ni ban ma bude baki ba a lokacin da ake gaishe gaishen.”
Ka ji fa matar aure ke kallon tumbin mijin wata, wai ba ta bude baki ba, ta ya za ta bude baki a yayin da kallon shigar bakar kwat ya dauke mata hankali, baki ba zai budu ba tunda an tsaya kallon tumbi.

“Allah mai Juyin Lamari, kwatsam rannan sai aurena ya mutu. Hakan ya sa na sami kaina da komawa birnin cigari da zama domin a can uwata da yayana suke.

Kwatsam wata rana ina duba sakwanni na asusuna na WhatsApp sai na ci karo da wani sako. Hotona aka dauko hoto daga ‘ standing’ dina aka turo min tare da rubutu kamar haka ‘ Gaskiya Hajiya kin iya saka janbaki’
Lambar babu suna , don haka sai na bude hoton da aka saka a DP din. Ga mamakina sa na ga hoton Goga!”
Gogan nan fa ba karamin shege ba ne. Ka ji wani Salo kuma na yabo da ya bullo da shi. Abin burgewar kawai shi ne a labarin babu wajen da ta fadi ya taba fada mataa irin Wannan sai bayan rabuwar aurenta.

Na yi zaton Magashi za ta yi blocking lambar Goga a matsayinsa na Wanda bai da mutunci, amma bari ka ji GOGUWAR.
“Sai na fara adana lambar da sunanshi sannan na ba shi amsa da cewa ‘Amma ba Wannan ne karo na farko da ka ga hotona mai dauke da janbaki ba. Me ya sa ba ka taba yin furucin ba sai yau.”
Dan Allah me Wannan amsar ke nufi ? Goga ya yaba ne domin ba ta da aure a lokacin, amma ita ta na tuhumar sa a baya me ya sa bai yaba ba. Kenan lokacin da take da aure. Da ace hukunci za mu yi sai mu ce Goga ya fi Magashi kiyayewa, wai kuma sai ta CE. “Na fadi haka ne saboda dama can ni uwar iya kwalliya ce, musamman saka Jan baki . Raayina ne yin kyale kyale, da shi na tashi kodayeke kusan duk Matan Kadoji suna da son gyaran jiki Wannan ya sa wasu ke kallon mu kamar ‘yan bariki, kodayake Kadoji ka zo na zo ce.”
Me ka fahimta a Wannan gaba. Ta nuna ita fa ta saba kwalliyarta, kwalliyar da wasu ke kallon ta kamar yar bariki ita da mutanen garin su Yan kazo na zo. Babu bukatar mai Nazari ya fashin wannan bakin, Jarumar ta yi kidanta ta yi rawar ta yadda kowa zai fahimta.

“Amsar da Goga ya ba ni bayan ya ga sakona ita ce: ” Na sami labarin aurenki ya mutu kuma yanzu haka kin dawo jihar mu ta cigari da zama Ba ki da nauyin kowa, shine dalilin yin maganata.”
Bawan Allah Goga. Wato sai da aure ya mutu ya fara magantuwa. Babu wajen da Jarumar ta fada mana ko da wasa ya tura wani sako a lokacin zaman aurenta. Duk da ta dauki Goga Mara mutunci bari ka ji me ta ce.

“Guntun Murmushi na yi domin tabbas abinda ya fada haka ne ”
Wato ta yi farin cikin samun sakon Goga. Wannan shi zai sa ka yarda maganata ta baya cewar dirin Goga fa ya tafi da zuciyar Magashi.

“Na Ba shi amsa kamar haka “Da gaske ne abinda ka fada, sai dai har yanzu ban gama idda ba. Ina bukatar takaita hira da kowanne namiji. Amma kar ka zata ko ina nufin ka ce kana so na.”
A Wannan bagire abin lura shine amsar da Magashi ta ba Goga akwai tausasawar kada ya yi fushi, ya dan jira ta gama idda yadda zai zama ba a sabawa sharia ba wajen zuwa wajenta. Amma har zuwa yanzu babu wajen da ta nuna tana bukatar yanke alaka ko nisanta da shi.

“Bayan an dauki satittika, sai Na kuma samun sakon Goga, inda ya ce “Hajiya a wace unguwa kike ne? Zan kawo miki ziyara a gaisa in kuma jajanta miki.
Na yi nazari kuma na ba wa kaina damar barin Goga ya ziyarce ni. Don haka sai na fada ma sa unguwar mu tare da kwatancen layinmu. Abin Mamaki, ba a fi minti Ashirin ba sai ga kiran Goga ya ce ” Ga ni a layin, Na yi Mamaki a raina na ce kamar mai jira.

Na sake kwatanta masa har ya karaso gidanmu. Na fita na similar shi, yana tsaye a jikin motarsa sanye da bakin yadi. Ya kura mini wani irin kallo da kwalakwalan Jajayen idanunsa. Ni sai a ranar ma na lura da cewa yana da Zane uku-uku a kumatunsa irin na mutanen jihar Gombe. Ashe dai tabbas Dan Gombe ne.”
To kun ji fa an ba da adireshin Goga kuma ya karasa. Sai a ranar ta ga uku-ukun fuskarsa. Wato duk haduwar da suke a taro ba ta taba lura ba, ita tumbi da belt ta fi lura da su, wadannan su su ka fi damun ta ba fuskar Goga ba. Zane uku-uku a kumatu hakika zanen Fulanin Gombe ne musamman Na Dikko, hatta Sarkin Gombe Na yanzu da Wanda ya rasu da duk wani bafulatanin asali a Gombe suna da one eleben.

Shi mutum idan har an fahimci bai da daraja da kima, bai da mutunci nesanta kai ake da shi, ko namiji ko mace, amma a labarin Jarumar kullum kara likewa Gogan take yi. Ban tunanin tana da wata hanya ta wanke kanta da nuna tsarki idan har Goga ya kasance ba mai tsarki ba. Zai zama Abokin Damo Guza.

Na so a ce an karashe labarin nan, domin sharhin zai fi daukar hankali da kara fito da hotunan yadda mu’amalar Goga da Magashi ta kasance. A Wannan lokaci ne za a fahimci wane ne Goga wace ce Magashi.

KARIN HASKE GA JARUMA
Nan Gaba Yadda ake yi da farko ba za ki taba nuna kin fahimci halayyar Goga ta rashin daraja ba, sai ki nuna Goga ya bullo miki a wani salihin mutum har ki amince da shi dari bisa dari, sai bayan tsawon lokacin da ya fara zuwa wajen ki ya fara wasu kalamai ko mu’amaloli na rashin daraja. Kina bayyana hakan kuma sai ki sauri ki nuna kin rabu da shi a Wannan sakamakon. Kowa zai ji tausayi kuma za a amince da ke, amma a ce farkon haduwa kin fahimce shi, kuma shekara da shekaru kika ci gaba da hulda da shi, sai daga karshe kuma ki zo da wani batu kowa zai dauka ruwa ba ya tsami banza akwai abinda ya hada Goga da Goguwa.

- Advertisement -