Sharhin Fim Din ‘Ci Da Addini’

0
85

Sharhin Fim Din ‘Ci Da Addini’

Daga: Musa Ishak Muhammad

Suna: Ci Da Addini.

Labari: Musa Mai Sana’a.

Tsara Labari: A. U Usman.

Kamfani: Mai Sana’a Leisure Kano.

Daukar Nauyi: Usman MaiLere

Shiryawa: Auwalu Abdullahi.

Bada Umarni: Musa Mai Sana’a.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Musa Mai sana’a, Bashir Na Yaya, Sani Garba SK, Baba Labaran, Lubabatu Madaki, Maryam CTB da sauransu.

Fim din Ci Da Addini, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani malami(Musa Mai Sana’a), wanda ya maida harkar addini sana’arsa. Shi wannan malami dalibai ne da shi a makarantar allo amma gabadayansu kasuwanci ya ke da su. Domin kuwa tura su ya ke su je su samo masa kudi koma ta wacce hanya ne su kawo masa. Babu ruwansa da karatunsu ko tarbiyarsu. Sannan har masallatai ya ke bi ya na neman taimakon mutane, ya na fada mu su wai dalibai gareshi photo voltaic fi karfin rikonshi don haka a taimaka masa. Kuma sannan shi wannan malamin ya na da ‘ya a gidansa wacce ta buwaye shi, ta fi karfin kulawarsa. Domin kuwa ta na barin gida a duk lokacin da ta ke so, kuma sannan ta dawo a lokacin da ta ke so.

A daya bangaren kuma a cikin fim din an nuna yadda a ke safarar yara mata daga karkara zuwa birni da sunan sama mu su aiki a gidajen masu kudi, amma sai a fake da saka su cikin harkar karuwanci da kuma lalata rayuwarsu. Sannan akwai wani bawan Allah (Bashir Na Yaya) kullum aikinsa kenan, ya yi ta tura yaransa birni domin gudun kar ya ciyar da su. Mazan ya tura su birni da sunan almajiranta, matan kuma ya tura su da sunan aikatau. A hakan ne namijin ya zo ya fi ya fi karfinsa bayan ya dawo daga almajirancin, sannan ita kuma macen a ka yi mata ciki a gidan da ta ke aiki. Amma da ya je maimakon ya nemi hakkinta, sai ya fake da cewa wai a bashi kudi a sakamakon abunda a ka yi wa ‘yarsa.

Mahimancin Taimako

A karshe dai shi malami (Musa Mai Sana’a) ‘yan sanda photo voltaic zo har gida photo voltaic kama shi, sakamakon wata harkalla da almajirinsa ya je ya ya kulla, a ka zo kuwa har gida a ka kama shi a ka tafi da shi.

Abubuwan Yabawa

Sunan fim din ya dace da labarin fim din.
An samu sauti mai kyau a cikin fim din.
An nuna illar sadaukar da ‘ya’ya don gudun talauci.
An nuna muhimmancin wadatar zuci.
An nuna illar rashin bibiyar yara idan an tura su karatu.
An nuna irin kalubalen da ‘ya’ya mata ke fuskanta a gidajen masu kudi da sunan yin aiki.

Kurakurai

Ba a nuna nadama ga malamin nan ba, duk da irin abunda ya aikata.
An samu kwan-gaba-kwan-baya a wajen tsarin labarin fim din.
Ba a nuna Ci Da Addinin sosai ba da a ka kira fim din da shi a cikin fim din.
Fim din ya rasa cikakkiyar alkibla.
An samu matsalar hotuna a wasu guraren.

Karkarewa

Fim din Ci Da Addini ya samu nasarori da yawa, da kuma wasu kalubalen da ba za a rasa ba. Fim din ya yi kokarin zuwa da wasu sakonni da su ke damun al’umma. Sai dai ba a tsara sakonnin yadda za su jewa mai kallo cikin sauki da kuma yin tasiri a kansu ba. Amma dai fim din ya samu nasarori kamar yadda mu ka fada a sama.

What's On Your Mind?