Shantalelliyar Budurwa Lauya Ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare

0
76

Wata kyakkyawar lauya mai daukaka tayi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wacce ta janyo cece-kuce.

Budurwar mai suna Barrister Khadijah Umar, mai amfani da suna @Barrkhadijah, ta ce rayuwa babu miji bata da dadi, komai nasarar da mace ta samu a rayuwa.

Shantalelliyar Budurwa Lauya Ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare

Wannan wallafar ta ta ci karo da ta wasu mata wadanda suke nuna cewa macen da take samun fiye da N500,000 duk wata, bata bukatar namiji a rayuwarta.

Kyakkyawar lauyar ta nuna cewa kudi ba matsalarta bace, namiji ne kadai matsalarta. Kamar yadda ta wallafa, “Ina bukatar namijin da zamu dinga cin kudina tare da shi.

Mace-macen da aka yi a Kannywood cikin 2020

Kamar yadd Legit na ruwaito.Wannan wallafar ta janyo cece-kuce iri-iri inda wani abba_dra cewa yayi: “Eh! Kuma duk wani namiji mai hankali, dukiya, ilimi, nasara da daukaka, akwai wata mace wacce ta tsaya masa. Dole mutum ya dogara da wani.”

Mubaraksaba1 ya ce: “Haka rayuwa take ‘yar uwa, yau da gobe sai Allah. Allah ya taimakemu.”

Wata UmeorizuP ta ce: “Mu din dai muke korafin cewa bamu bukatar namiji, yanzu kuma mun samu daukaka muna bukatar namiji. Toh, ga dai mu nan.”

What's On Your Mind?