SEMA Ta Bukaci Goyon Baya Da Hadin Kan Al’ummar Jihar Yobe

- Advertisement -

SEMA Ta Bukaci Goyon Baya Da Hadin Kan Al’ummar Jihar Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), Dr. Mohammed Goje ya bukaci cikakken hadin kai da goyon bayan al’ummar jihar dangane da ayyukan da hukumar su ta sanya a gaba na tallafin gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ya ce aiki ne wanda samun nasarar sa sai ta hanyar jama’ar jihar.

Ya ce hukuma ce wadda ayyukanta ba a sanya musu rana balle lokaci, kana kuma ya ce SEMA hukuma ce a karkashin gwamnatin jihar Yobe amma kuma ta na aiki da kungiyoyi da daidaikun masu bayar da agajin gaggawa, wanda a lokuta da dama su kan zabi bangaren da suke da sha’awar bayar da tallafi tare da adadin da suke da muradi, sabanin abinda wasu ke tsammani.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan a sa’ilin da yake zanta wa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Damaturu babban birnin jihar Yobe, da yammacin ranar Talata, tare da sanar da cewa suna iya kokari wajen ganin solar kwatamta adalci da gaskiya kamar yadda al’ummar jihar ke musu fata.

Har wala yau ya shaidar da cewa SEMA ta na aiki babu dare babu rana tare da sauran kungiyoyi takwarorinta domin ganin samun nasarar ayyukan da aka sanya a gaba na ayyukan jinkai a kowane bangare da yanayin rayuwar al’ummar jihar Yobe.

A hannu guda kuma ya yaba da kokarin Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni bisa ga cikakken goyon bayan da ya dace ga hukumar, “Bari na sanar daku wani abu da ya faru kwanan nan, baya ga yadda muka fuskanci karancin kayan abinci a wuraren ajiyarmu, hakan ya sanya na sanar da Maigirma Gwamna halin da ake ciki, wanda nan take ya ba mu umurnin cewa mu je ma’ajiyar kayan amfanin gonarsa mu debi dukan kayan abincin da yake a wajen, wanda ko shakka babu wannan babbar sadaukarwa ce ga al’ummarsa. Daga baya kuma ya turo mana da gwamman motocin abinci daga Abuja.”
A gefe guda kuma shugaban hukumar ya nemi taimakon yan jarida wajen samun nasararsu tare da kwarmata musu duk wata matsalar da suka hango domin gyara a kokarin yi wa al’ummar jihar hidimar da ta dace, “Saboda kowane lokaci kofarmu a bude take gareku kuma zamu karbi gyara da shawara ko wasu bayanan da zasu taimaka mu habaka ayyukan mu. Saboda kusancin da kuke dashi ga jama’a a matakin farko, sannan kuma al’umma tana da aminci daku.” In ji shi.

- Advertisement -